Ƙasar Sin na son ɗaukaka haɗin kai, abota, haɗin gwiwa da ƙasashen Musulmi zuwa wani sabon matsayi

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya bayyana a jiya Talata cewa, ƙasarsa a shirye take ta ɗaukaka haɗin kai, da abokantaka da haɗin gwiwa da kasashen musulmi zuwa wani sabon matsayi.

Wang Yi ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake ganawa da babban sakataren ƙungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Hissein Brahim Taha a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan yayin da ya halarci zaman majalisar ministocin harkokin wajen ƙungiyar ta OIC karo na 48.

Wang ya ce ƙungiyar OIC dake wakiltar haɗin kai da ’yancin ƙasashen musulmi, ta zama wata gada ta raya dangantakar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen musulmi.

Jami’in na ƙasar Sin ya ƙara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kiyaye ‘yancin kai, da cikakkun yankunan ƙasashen musulmi, tare da nazarin hanyar samun ci gaba mai dacewa da yanayin ƙasashen. Haka kuma, ƙasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da dukkan ƙasashen musulmi.

Ya ce, ƙasar Sin za ta ba da ƙarin alluran rigakafin COVID-19 miliyan 300 ga ƙasashen musulmi, tare da tallafawa ƙasashe mambobin ƙungiyar OIC a Afirka wajen yakar annobar.

Wang ya kara da cewa, ƙasar Sin za ta inganta haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu a fannin ilimi da horaswa, tare da shirya taron ƙarawa juna sani karo na biyar game da shawarwarin wayewar kan Sin da musulunci.

A nasa jawabin, babban sakataren ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi ta OIC Hissein Brahim Taha, ya yiwa Wang Yi maraba a madadin ƙasashe mambobin ƙungiyar OIC fiye da 50. Yana mai cewa, halartar taron da Wang Yi ya yi, zai ƙara inganta hulɗar dake tsakanin ɓangarori biyu.

Fassarawa: Ibrahim Yaya