Ƙidayar shekarar 2023 hanyar magance talauci da rashin tsaro ce a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ƙidayar al’ummar ƙasa da za a yi a shekara mai zuwa a Nijeriya za ta taimaka wa gwamnati wajen yaƙi da talauci da kuma rashin tsaro.

Shugaban ƙasar ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a taron masu ruwa da tsaki a kan ƙididdigar al’umma da ta gidaje na ƙasa gabaɗaya wanda aka gudanar a Abuja.

Wannan bayani yana ƙunshe ne a cikin wani jawabi wanda kakakin fadar shugaban ƙasar mai suna Femi Adesina ya sanya wa hannu.

Buhari ya ƙara da cewa, hasashe ya nuna cewa, Nijeriya za ta samu matsayin ƙasa ta uku a fanni yawan al’umma nan da shekarar 2050.

Wato za ta rufa wa Indiya da Chana baya, kamar yadda wani rahoton sakamakon sashihiyar kuma nagartacciyar ƙidayar ya bayyana.

Don haka a cewar shugaban, Nijeriya tana buƙatar yin waccan ƙidayar domin ta san yadda za ta tsara wancan ƙaruwar al’ummar da aka yi hasashe. Domin kawar da matsaloli kamar na rashin tsaro da suka fi addabar jama’a.

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa, yana saran wannan ƙidayar da za s gudanar a baɗi ta gidaje da al’umma ta zama ma fi sahihancin da kuma ba da sakamako mafi kyau.

Domin a cewar sa, ƙidayar da aka yi tun shekaru 16 baya wato tun shekarar 2006, har yanzu akwai giɓin da ba a cike ba.

Sannan kuma ta yi tsufa da yawa a ce za a cigaba da amfani da sakamakonta wajen tsara rayuwar ‘yan Nijeriya. Hakan ya faru ne sanadiyyar ƙin gudanar da ƙidayar da aka yi a ƙasar na tsahon waɗancan shekaru.

A don haka, shugaban ya ce ya zama dole a gudanar da sabuwar ƙidayar saboda a samu sahihin sakamako abin dogaro wajen shirya tsarin samar da cigaban al’umma. Domin sanin yawan al’umma yana da alaka da irin ayyukan da za a yi musu.

Sakamakon ƙidayar da aka gudanar a shekara ta 2006 ya nuna adadin al’ummar Nijeriya sun kai ƙiyasin 216,783,381, wato a halin yanzu tana a matsayin ƙasa ta 6 ma fi yawan alumma. Kuma ita ce ƙasa mafi yawan al’umma a yankin Afirka gabaɗaya.

A cewar sa ma Nijeriya ta karya shawarar da ƙasar Amurka ta ba da na yin ƙidayar bayan kowacce shekara goma.

Daga ƙarshe Shugaban ya nemi masu ruwa da tsaki a harkar ƙidayar da su mara masa baya don samun nasarar atisayen.

Wato gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi, mazavu, masarautun gargajiya da na addini, ma’aikatu masu zaman kansu, kafafen yaɗa labarai, masu ba da tallafi da kuma dukkan al’umma don su ba shi haɗin kai don gudanar da ƙidayar shekarar 2023.