Ɗan takarar sanata na APC a Jigawa ya rasu

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHIR

Ɗan takarar sanata na Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya, wanda ke neman wakilcin mazaɓar Jigawa ta Tsakiya a zaɓe ami zuwa ya rasu.

Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya da ya yi wanda aka kwantar da shi a Asibitin Nizamiye da ke Abuja.

Cikin sanarwar da Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru ya fitar ya aike da saƙon ta’aziya ga ‘yan uwa da iyalan mamacin inda ya bayyana marigayin a matsayin ɗan kishin ƙasa abun koyi ga matasa masu tasowa.

Gwamna Badaru ya ƙara da cewa, “Duk da ita mutuwa dole ce amma muna masa kyakkyawan zaton ganin irin doguwar jinyar da ya yi fama da ita muna fatan Allah Ya sa mu ma mu cika da imani.”

Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya shi ne ɗan takarar jam’iyar APC ɗaya tilo da zai wakilci Jam’iyyar a zaɓen 2023 a Dutse.

Haka kuma, shi ne tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Dutse/Kiyawa.