Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta yi sabbin shugabanni

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen Jihar Kano, wato Association of Nigerian Authors (ANA) ta yi sabbin shugabanni da ya biyo bayan taron da ya gudana a ɗakin karatu na Murtala Muhammed ranar Lahadi da ta gabata.

An dai yi zaɓen ƙungiyar ne yayin gabatar da manyan taruka da ta saba gudanarwa duk ƙarshen wata.

An kuma zavi Dr.Murtala M. Uba wanda malami ne a sashen ilimin nazarin ƙasa wato (Geography) da ke jami’ar Bayero Kano a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

Jim kaɗan bayan kammala zaɓen ne dai, sabon shugaban Dr. Murtala Uba ya ce, za su jagoranci wannan ƙungiya zuwa tafarki mafi dacewa ta kowane ɓangare tare da haɗin kan mambobin ta musamman shugabannin da suka gabata duk da cewa tun kafuwar ƙungiyar ake ta ƙoƙari wajen ganin an kai ta mataki wanda duniya za ta yaba mata duba da manyan masana da ƙwararru a fannin ilimi da take dashi amma hakan ya ci tura.

“Ina tabbatar maku da cewa a wannan lokaci na shugabancinmu za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa ƙungiyar marubuta a Jihar Kano ta zama guda cikin manyan ƙungiyoyi da za ayi alfahari da ita.”

Da yake nasa jawabin, sabon PRO na Hausa Bashir A. Bashir, (Influencer) ya ce duk, da yake cewa gwamnati bata tuna su a matsayin masu bai wa al’ummar Jihar Kano gudunmawa wajen kawo sauye-sauye a zamantakewar al’umma ba, duk da haka ya jaddada aniyar su ta cewa ƙungiyar marubuta ta ANA za ta zama zakaran gwajin dafi wajen kawowa al’ummar Jihar Kano cigaba musamman ɓangaren ilimi da rubuce-rubucen da zai canzawa matasa maza da mata tunani mai amfani.

An dai zaɓi Dr. Murtala M. Uba a matsayin Shugaba, sai mataimakin sa Malam Kamilu Dahiru Gwammaja, ya yinda aka zavi, Ibrahim M. Indabawa a matsayin Sakataren, aka kuma zaɓi Aliyu Abdullahi (Abal Hassan)a matsayin mataimakin sakataren, sai kuma Ma’aji aka zavi Sadiya Garba. Sakataren Kuɗi kuwa aka zaɓi Hassan Ibrahim Gama.

Kazalika an zaɓi mai magana da yawon ƙungiyar wato PRO a ɓangaren Hausa shi ne Bashir A. Bashir (Influencer), sai mai magana da yawon ƙungiya na Turanci a ka zavi Abba Musa Idris, an kuma zaɓi Sani scholar jami’in walwala, sai mai binciken kuɗi a ka zaɓi Ayyuba Muhammad Danzaki

Mataimakiyar mai binciken kuɗi kuwa Aisha Aliyu Jibril aka zava, sai Jibrin Adamu Rano a matsayin mai bada shawara kan shari’ar.

Sannan an zaɓi shugabanni marasa gafaka da suka haɗa da: Zubairu M. Balannaji da Mukhtar A. Gandu da Mazhun Idris da Tijjani M. Musa.

Taron ya samu halartar lambobin wannnan ƙungiya da manyan malamai daga manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan.