Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa, Janar Abubakar Abdulsalami (rtd), ya yi kira ga jam’yyun siyasa da magoya bayansu da a guji nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu yayin zaɓen gwamnonin da za a gudanar ranar Asabar a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo.
Abdulsalami ya yi wannan kira ne yayin da jam’iyyin siyasa su 18 da za su fafata a zaɓen gwamna a Jihar Kogi suka rattaɓa hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya ranar Laraba a jihar.
Da yake jawabi ta bakin wakilinsa Cardinal John Onaiyekan, tsohon shugaban ƙasar ya ce: “Wannan taro na da muhimmanci saboda lamarin zaɓe a Nijeriya ya zama na a-yi-rai-ko-a-mutu wanda hakan ba alheri ba ne ga ƙasa da al’ummarta.”
Kazalika, Abdulsalami ya yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta yi adalci a zaɓen da za a gudanar.
Ya ce zaɓuɓɓuka a Nijeriya za su gudana cikin lumana muddin masu ruwa da tsaki kowa ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Ya ƙara da cewa, lokaci ya yi da ya kamata ‘yan takara su gabatar da kansu wajen jama’a don neman zaɓe maimakon ɗauki-ɗora tare da danne wa masu kaɗa ƙuri’a ‘yancin zaɓen wanda suke so.
A nasa ɓangaren, Bishop Mathew Hassan Kukah wanda ya samu wakilcin Attah Barkindo a wajen taron, ya buƙaci ‘yan siyasa kowa ya natsu domin a samu zaɓe ya gudana cikin ruwan sanyi.