Kowa ya yi rubutu mai kyau zai samu karɓuwa – Ado Ahmad MON

“Kyakkyawar mu’amala da mutane tasa ake karrama ni”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Sunan Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) Sani Mai Nagge, ba ɓoyayye ba ne a duk faɗin ƙasar nan, ba ma tsakanin marubuta da masu shirya finafinai ba, har ma da manazarta na ƙasa da ƙasa. Ya yi rubuce-rubuce da dama cikin harsunan Hausa da Turanci, a ciki har da littafin da yanzu haka ya shiga cikin manhajar koyar da Hausa a manyan makarantun sakandire na qasar nan. Ya samu shaidar karramawa iri-iri da suka jawo masa ɗaukaka a duniya fiye da duk wani marubucin Hausa. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, fitaccen marubucin kuma jarumin shirin ‘Kwana Casa’in’ na tashar Arewa24 ya bayyana ƙoƙarin da yake yi na juya wasu daga cikin littattafansa daga rubutun boko zuwa Ajami, da yadda yake rainon wasu marubuta zuwa matakin da duniya za ta yaba da baiwarsu.

MANHAJA: Za mu fara da jin cikakken sunanka da taƙaitaccen tarihinka.

ADO AHMAD: To, Alhamdulillahi. Ni dai cikakken sunana shi ne Ado Ahmad Gidan Dabino, MON. Ni marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, sannan kuma mai shiryawa da bayar da umarni, jarumi a masana’antar Kannywood, kuma ɗan jarida.

An haife ni a shekara ta 1964 a garin Ɗanbagina da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Na taso a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Na fara karatun allo, (Alƙur’ani) a makarantar marigayi Malam Rabi’u a Unguwar Zangon Barebari, a shekarar 1968 da karatun littattafai na Islamiyya a makarantar marigayi Sheikh Tijjani na ‘Yanmota a 1971.
Ban samu damar yin karatun boko ina ƙarami ba, sai da na girma, sannan na shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci wato Adult Evening Classes Kano, a shekara ta 1984 zuwa 1986. Na yi makarantar sakandire ta dare da ake kira da G.S.S. Warure Evening Session a shekara ta 1987 zuwa 1990.

Na kuma shiga Jami’ar Bayero, inda na samu shaidar Diflomar ƙwarewa a kan yaxa labarai, wato Professional Diploma in Mass Communication a Sashin Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005.
Na kasance marubuci, kuma manazarci, inda na gabatar da muƙalu da dama a tarurrukan ƙara wa juna sani a cikin Nijeriya da ƙasashen waje. Ina kuma yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujallun Hausa.

Tare da ni aka kafa wasu ƙungiyoyi, kamar ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jihar Kano, (ANA) a shekara ta 1992, kuma na riƙe shugabancinta na tsawon shekara uku, da ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, wato Kano State Filmmakers Association, wanda a halin yanzu ni ne shugaban riƙo na ƙungiyar. Akwai kuma ƙungiyar marubuta ta Raina Kama, wato Raina Kama Writers Association, wanda har wa yau ni ne shugabanta.

Na taɓa gabatar da shirin Alƙalami Ya Fi Takobi, a gidan rediyon Freedom Kano, da kuma shirin Duniyar Masoya a gidan rediyon Shukura FM da ke Damagaram, a Jamhuriyar Nijar.

Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba ni damar zuwa ƙasashe fiye da goma sha biyar na Afrika, sannan kuma a ƙasashen Turai ya samu zuwa ƙasashen Ingila da Faransa da Italiya da Holland da kuma Jamus.

Na zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009, ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir ƙaraye, a Abuja. Na samu takardun yabo da dama daga jami’o’i da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummawa iri-iri da nake bayarwa waɗanda suka shafi harshen Hausa, adabi da al’adu ta fannin rubuce-rubuce da shirin finafinai da aikin jarida da harkokin ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati.

A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 na samu takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha ɗaya da aka yaba da su a Jihar Kano wajen bayar da gudunmawa game da cigaban al’umma.
Sannan a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama ni da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da yake yi a cikin ayyukansa.

A shekarar 2017 na samu zuwa matsayin tantancewa ta ƙarshe (nomination) a gasar finafinai ta Zuma Film Festival da ke Abuja a matsayin jarumin jarumai na Afrika. A shekarar 2018 na samu nasarar lashe kambin jarumin jarumai har sau uku a cikin gasar AMMA Award da Kaduna International Film Festival da Arewa Entertainment, sannan na amshi kambun mai shirya finafinai da ya zarce kowanne (Best Producer) a ‘KILAF Film Festival’ duk a cikin fim ɗin Juyin Sarauta. A shekarar 2019, na sake zama jarumin jarumai (Best Actor in Leading Rule) sannan na amshi kyautar alqalan gasa (Golden Jury Award) a gasar Kaduna International Film Festival.

Ina cikin wasu ƙungiyoyi kamar haka: Motion Pictures Practitioner’s Association of Nigeria, (MOPPAN) da Association for Promoting Nigerian Languages and Culture, (APNILAC) da West African Research Association (WARA) da Indigenous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) da sauransu.

A ƙarshe kuma ni ne Shugaba kuma Daraktan Gudanarwa na kamfanin Gidan Dabino International Nigeria Limited.

Lura da irin waɗannan ɗimbin nasarori da ka samu a duniyar adabi da finafinai, kana ganin menene sirrin samun wannan ɗaukaka taka?

Haƙuri da juriya da kuma zama lafiya da mutane da kyautata mu’amala tsakanin marubuta da masu sana’ar fim da sauran jama’ar gari masu kallo da karanta littattafai.

A baya an san ka da rubuce-rubuce littattafan soyayya da waƙoƙi, me ya kawo ka canza akalar rubutunka zuwa littattafan wasan kwaikwayo da na ƴan makaranta?

Abin da ya sanya haka, dama ina da basirar rubuta littafin wasan kwaikwayo kuma na ga babu wadatarsu a kasuwa, ba kowa yake rubuta littafin wasan kwaikwayo ba, haka ma karatawa, mafi yawa sai ɗaliban da aka sanyawa a manhajar koyarwa ne suke nemansa, kuma babu wadatarsa, shi ya sa na ce bari na mayar da hankali can don in daɗa a rumbun adabin rubutaccen wasan kwaikwayo.

Akwai wasu littattafanka da Hukumar Shirya Jarrabawar Fita Sakandire ta WAEC ta amince a riƙa amfani da su wajen koyarwa a Hausa, wanne mataki aka bi har aka cimma wannan nasara?

Abin da ya faru, a matsayina na mai kamfanin wallafa littattafai, an kira ni daga Hukumar WAEC daga Lagos ana neman wasu littattafai na zube, sai na aika da littattafan mutane biyu, na Dr. Bukar Usman, OON da na marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa, suka zavi na Bashir Tofa, mai suna ‘Gajerun Labarai’, suka sanya a manhajar koyarwa. Bayan shekara ɗaya kuma, an sake kirana ana neman littafin wasan kwaikwayo, na aika da Malam Zalimu da Daƙiƙa Talatin, a qarshe aka zaɓi Malam Zalimu, aka sanya shi a manhajar koyarwa ta babbar sakandire ta aji na 1 da na 2 da na 3 daga shekarar 2023 zuwa 2026, sannan za a karanta shi a jarabawar WAEC da NECO da JAMB a shekarar 2026 zuwa 2030.

Menene ya ja hankalinka ka ga ya dace ka shigar da littattafanka daga hannun masu karatu na gama-gari zuwa ga ɗalibai da ke ajujuwa?

Ba ni na nema ba a saka ba, amma dai in ka yi abu mai kyau zai samu karvuwa a kowanne vangarori na al’umma, ai ka ga ana karantawa a manyan makarantu daga jami’o’i zuwa kwalejojin ilmi na arewacin Nijeriya. Saboda haka wannan ina ganin shi ne dalili, wato ka yi abu mai inganci za a amshe shi a yi amfani da shi.

Waɗanne littattafai nan gaba ka ke shirin fitarwa don ƴan makaranta, kuma kawo yanzu nawa ka buga?

A halin yanzu ina da sababbin littattafai guda huɗu da za su fito nan gaba, ‘Taskar Fasaha’, ‘Rubutattun Waƙoƙi’ da ‘Ina Mafita’, wasan kwaikwayo da ‘Gani Da Ido Maganin Tambaya’, littafin labarin tafiye-tafiyena a ƙasashen duniya guda ashirin, da kuma littafin ‘Rabuwa’ labarin wata soyayya ta gaskiya da aka yi a tsakanin ƙasashen Faransa da Amurka, Nijar da Nijeriya.

Kana ganin sauran marubuta ma za su iya shiga wannan fage, duba da yadda kasuwancin littattafai ya mutu?

Mai zai hana su iya shiga in dai za su yi rubutu mai ma’ana da inganci!Ai wani lokacin in ka yi rubutu ko ba ka nemi a sanya a manhaja ba, ana iya sanyawa ba tare da ka nema ba, saboda ya cancanta a sanya shi, kamar yadda aka yi wa nawa da na Bashir Tofa.

Shin yaya ka ke ƙoƙarin taskace littattafanka na baya, ganin wasu marubutan na kukan ɓacewar littattafansu a kasuwa da gida?

Ni duk littattafaina na killace su waje guda babu wanda ban da shi a cikin kwamfuta, kuma babu wanda ban da bugaggensa. Yanzu ka ga littafin ‘In Da So Da Ƙauna’, an haɗe na 1 da na 2 tun a shekarar 1991. An kuma haɗe littafin ‘Hattara Dai Masoya’ na 1 da na 2 a 1992. Akwai kuma ‘Masoyan Zamani’ na 1 da na 2, wanda aka buga a shekarar 1993, shi ma an haɗe su waje ɗaya. Ga ‘The Soul of My Heart’, fassarar littafin ‘In Da So Da Qauna’ na turanci. ‘Wani Hanin Ga Allah’ ma an haɗe shi waje guda daga na 1 da na 2.

Sannan an fassara littafin ‘Masoyan Zamani’ zuwa turanci, da aka sa wa suna ‘Nemesis’ a shekarar 1995. Akwai littafin ‘Kaico!’ wanda ya fito a shekarar 1996. Na kuma wallafa littafin ‘Duniya Sai Sannu!’, a 1997. Littafina na Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan wanda muka yi masa aikin haɗin gwiwa ni da Sani Yusuf Ayagi ya fito ne a 2004. Sai kuma littafin wasan kwaikwayo na ‘Malam Zalimu’, da ya fito a shekarar 2009.

Ina kuma da wani littafin turanci mai suna From Oral Literature To Video: The Case of Hausa Literature, wanda wasu fitattun masana adabin turanci Joseph Mclntyre da Mechthild Reh, suka duba shi a 2011. Na yi littafin Mata Da Shaye-Shayen Kayan Maye: Ina Mafita? a 2012, da littafin Daqiqa Talatin a 2018, an kuma fassara shi zuwa turanci wanda aka sa wa suna Young Women Substance Abuse: The Way Out.

Kana da shaidar karramawa ta ƙasa ta MON da ake bai wa jajirtattun ƴan qasa da suka yi fice a wani fanni, wanda babu wani marubucin adabin zamani da ya taɓa samu, mene ne ka ke ganin ya jawo hankalin hukumomi a kanka?

To, ban sani ba gaskiya, amma dai abin da na sani shi ne, kowa ya yi da kyau zai ga da kyau. Kuma an duba ayyukana na tsawon shekara talatin kafin a ba ni wannan lambar yabo ta ƙasa wato Member of the Order of the Niger (MON). Na fara rubutu ina da shekara ashirin a duniya wato 1984, an ba ni kyautar a shekarar 2014, lokacin na cika shekara hamsin a duniya. Saboda haka a dunƙule ina iya cewa duk abin da ka ke yi duniya tana gani, kuma watarana za ka samu sakamakonsa.

Wanne ƙoƙari ka ke yi na ganin sauran marubuta sun samu irin wannan gogewa da ɗaukaka a fagen rayuwa da siyasa, ta dalilin rubuce-rubucensu?

Muna yin iya abin da za mu iya, ta hanyar rainon wasu da ba su goyon baya da taimaka musu da abin da za mu iya taimakawa, da bayar da shawarwari da koyarwa da shirya tarukan ƙarawa juna sani. Da yin ayyuka na haɗin gwiwa.

Tsakanin rubuce-rubucen littattafai da shirya finafinai da ka ke yi wanne ya fi jawo maka farinjini a wajen jama’a?

Kowanne da matsayinsa. A rubutu aka fara sanina, kuma an fara sanina a wannan fage na rubutu tun shekarar da littafina na farko In Da So Da Ƙauna ya fito kasuwa a shekarar 1990. Shi kuma fitowa a cikin fim na fara ne a shekarar 1994, a cikin fim ɗin littafina na In Da So Da Kauna, wato bayan an sanni da shekara huɗu a fagen rubutun littafi. Saboda haka shaharata ta fi a rubutu a wancan lokacin daga 1990 zuwa 2009. Daga 2017 ne wata shaharar ta samu ta vangaren fim a sanadin fim din Kwana Casa’in da nake fitowa a ciki har zuwa yau. Saboda haka na iya cewa a littafi na fi shahara kafin na zo na yi shahara ta fim.

Gaya mana abin da ya zaburar da kai ka fara buga jaridar Hausa da rubutun ajami a maimakon da rubutun boko?

Wannan wani qoqari ne na haɗin gwiwa tare da Malam Bashir Yahuza Malumfashi da kuma sauran mutanen da ake ganin sunayensu a cikin jaridar domin a farfaɗo da darajar Ajami a Arewacin Nijeriya.

Shin wacce nasara aka samu bayan fitowar wannan jarida da ƙalubalen da ake fuskanta?

Mun samu nasarar daɗa zaburar da mutane da kuma tunasar da su cewa ashe za mu iya cigaba da amfani da Ajami a jaridunmu, kuma akwai masu son karantawa, kawai ba a yi ne, kuma ba a samun tallafi wajen buga jaridun ajami, wato ta hanyar samun tallace-tallace daga kamfanoni da hukumomi da ‘yan siyasa da kuma ɗaiɗaikun mutane.

Kana tunanin fitar da rubutun littafi da ajami nan gaba?

Akwai wannan tunanin in sha Allah.

A baya ka taɓa fassara wasu rubuce-rubucenka zuwa harshen turanci, me ya dakatar da kai daga cigaba da wannan fassara zuwa sauran littattafanka?

Kamar yadda na yi bayani a baya, an fassara littafin ‘In Da So Da Ƙauna’ zuwa ‘The Soul of My Heart’, a shekarar 1993. An fassara littafin Masoyan Zamani zuwa Nemesis, a shekarar 1995.

Daga baya kuma an sake fassara Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita? Zuwa Young Women Substance Abuse: The Way Out a 2019. Akwai kuma waɗanda aka fara fassarawa ba a gama ba kamar littafin Kaico! da Malam Zalimu.

Wanne ƙoƙari ku ke yi na samar da wata hanya ta tsaftace harkar rubutu daga marubuta masu amfani da batsa cikin rubuce-rubucen su?

Hanyar ita ce tarukan ƙarawa juna sani a fili da kuma na kafar sada zumunta. Da kuma bayar da shawarwari a fili, gaba da gaba. Da kiraye-kirayen da ake ta yi don nusar da masu yin hakan da nuna musu hakan ba shi da wata fa’ida a al’adarmu da rayuwarmu, illa gurvata zukatan matasa maza da mata.

Menene ra’ayinka game sabuwar hanyar wallafa littattafai ta hanyar yanar gizo da manhajojin sayar da littattafai na zamani?

Ra’ayina shi ne a yi, tun da Allah shi ne zamani, kuma yadda aka dama haka za a sha. Ai komai da lokacinsa. Kamar fim ne da ana yi a faifai iri-iri amma yanzu babu wannan tsarin kamar da, wata rana ma za ka ga an daina duk waɗancan hanyoyin an samo sababbi.

Wanne tunani ku ke da shi na ganin nan gaba an samar da wata cibiya ta nazarin rubuce-rubucen Hausa da shigar da su cikin tsarin bincike na jami’o’i da manazarta kan al’adu da tarihi?

Wannan wani babban tunani ne wanda yana da kyau, ko a yanzu za ka dinga jin sunayen cibiya kaza da cibiya kaza wadda ta shafi harshen Hausa da al’adu da tarihi da nazari, kuma tun da an fara samu, babu shakka ko muna raye ko ba ma raye watarana za a samar da wata babbar cibiya mai zaman kanta kwatankwacin wadda ka ke magana, ba wai ta cikin jami’a ba, a’a, ta wajen jami’a.

Menene saƙonka ga marubuta adabi na duniya bakiɗaya?

Saƙona, mu yi rubutu mai ma’ana, da ilmantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa, sannan mu kula da addininmu da al’adarmu a cikinsa, musamman mu Hausawa. Domin an ce adabi madubin rayuwa ne.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Raina Kama… ka ga gayya. Kamar yadda sunan ƙungiyarmu da muka kafa ta marubuta a Jihar Kano a wajajen 1992 zuwa 1994, wanda ni ne shugabanta. Sannan akwai wata karin maganar ma da yake ake a kaina, wato Ramin shuka ba tsayi sai albarka!

Masha Allah. Muna godiya ƙwarai da gaske.

Ni ma ina godiya.