Ƙungiyar matan Ƙadiriyya ta shirya bikin murnar Mauludi

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Naƙibatu Ƙadiriyya, Malama Baraka Fatima Adamu Ɗanfanta ta shirya gagarumin mauludi, inda ta jagoranci gangamin mata daga ƙungiyoyi daban-daban da kuma ɗaiɗaikun mata daga Kano da wajenta don taya ɗaukacin al’ummar musulmai murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyan halitta, Annabi Muhammadu (SAWW), wannan watan mai alfarma wanda aka gabatar a Unguwar yalwa da ke Goron dutse cikin birnin Kano a ranar lahadi da ta gabata.

A jawabin naƙibatul ƙadiriyya, malama Baraka Adamu Ɗanfanta ta ce, maƙasudin wannan taro shi ne jadada murna da farin ciki na samuwar wannan babban baiwa da Allah ya yi mana na aiko shugaban halitta na duniya da lahira wanda kuma shi ne yafi kowa daraja da ɗaukaka, don haka muna alfahari, ya zamana wajibi mu nuna cewa muna murna da farin cikin da zuwan ma’aikin Allah na duniya.

Musamman mu wanda Allah ya zaɓe mu ya sanya mu cikin al’uumarsa wanda suka fi kowacce sabo da albarkarsa, to ya zama dole mu zauna muyi mu sake karatun tarihinsa da halayyansa da jama’a ta ji abun koyi akan dukkan ɗabi’unsa da halayansa wanda duka abun koyi ne ga al’ummarmu. Haka kuma ta ja hankalin jama’a musamman mata kan yawaita alkairi biyayya ga mazaje da tarbiyyar yara da sauran al’umma.

A qarshe ɗaya daga cikin manyan baƙi, malama Zainab Sheik Ɗahiru Usman Baushi jagoran Ɗari’ƙar Tijjaniyya sautul Islam Malama Zainab ta bayyana farin cikin ta na cigaban da aka samu da yau mata ke shirya Mauludi gashi yau ƙadiriyya da Tijjaniyya da ma sauran al’umma an haɗu ana murnar Maulidi wannan cigaba ne a Musulunci.

Taron dai ya samu halattar iyalan marigayi Alhaji Ado Bayaro sarkin Kano, iyalan Khalifa sheikh Isyaka Rabiu da mai ɗakin Abba Kabir Yusif Abba Gida Gida da sauran mata daga sassa daban-daban na kano da wajenta.