LUFADA ta shirya taro a karon farko

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Ƙungiyar cigaban zuriyar Lulu (LUFADA), ƙarƙashin shugabcin Alhaji Abdulrashid Mansur Ashiru ta gudanar da gagarumin taro a karon farko wanda aka gabatar a ɗakin taro na gidan Mumbayya a Gwammaja cikin ƙaramar hukumar Dala ta Jihar Kano a ranar Lahadi ta makon jiya.

A jawabin shugaban ƙungiyar Alhaji Abdulrashid Mansur Ashiru ya bayyana cewa, maƙasudin wannan taro shi ne a cigaba da zamunci tsakaninsu kuma a cigaba da taimakawa juna a tsakaninsu kamar yadda ya kamata da kuma cigaban tarbiyya na wannan zuriya ta cigaban da nagarta kuma yanzu haka matasa 500 na zuriyar Lulu suka samu tallafin karatu da abun da ya shafi lafiya da sauransu.

Shi kuwa shugaban kwamitin aiwatar da taron sharuf Mustapha Sagir Lulu ya ce, wannan taro shi ne na farko kuma ya samu nasara duk da cewa wannan ƙungiyar ta haura shekara 20 amma irin wannan taro shi ne na farko wanda aka yi a irin wannan taro a matsayin gwaji kuma jama’a su ji su yi ko yi da tsarin wannan ƙungiya ta LUFADA watau Lulu Family Development Association da ke Kano.

Nazif Faruqu shi ne jami’in hurɗa jama’a na ƙungiyar ya ce, duk waɗannan ‘yan ƙungiyar na da ke kyakyawar mu amala a tsakaninsu da sauran al’umma a duk inda wannan zuriya ta Lulu ta ke a cewar Farfesa Nazif Faruƙu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *