Shaye-shaye a tsakanin matasa: Ina mafita?

Assalamu alaikum. Yau zan yi wasiƙa ne akan wata matsala da take neman fin ƙarfinmu. Za mu tattauna ne akan matsalar da kusan yanzu ta zama ruwan dare musamman a yankunan arewacin ƙasar nan. Haka zalika, kamar yadda muka sani ne cewa, Hukumar yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi (NDELA) na yawan cewa akwai buƙatuwar irin waɗannan kiranye-kiranyen.

Sai dai abin da mamaki ganin yadda mutane da kuma sauran iyaye ba sa iya ɗaukar kowane mataki don ganin an kawar da wannan mummumar ɗabi’ar. Kuma kowanne bigire kake walau talaka ko mai kuɗi, malami ko ma’aikaci kana da gudunmawar da za ka bayar a wannan fanni da daƙile shaye-shaye.

Ba wannan ba ma, kawai idan muka dubi al’ummarmu ta hausa mun san akwai abin da yake damunta wanda har zuwa yanzu an kasa magance ta. Shaye-shayen kayan maye daga matasanmu kusan matsalace leƙa gidan kowa, babu wata unguwa walau saƙo ku lungu, har ma da unguwannin ‘yan gayu da za ka ce wannan matsala ba ta damun su. Wannan ba shi ne wasiƙa na farko akan Illar shaye-shaye ga matasa ba, sai dai wasu kan ɗauka cewar Gwamnati ce kaɗai za ta iya kawar da wannan matsala, ni dai a tunani na ko mai idan muka ce sai Gwamnati ta yi, to lalle al’ummarmu za ta ci gaba da lalacewa kuma ba bu mai kuzarin kawo mana gyara.

Wannan matsala ce babu ɗan talaka, babu ɗan mai kuɗi, babu ɗan malamai, babu maraya babu mai gata, haka kuma babu mace babu namiji, ta shafi kowa, babu mai karatu babu mara ilimi, hantsi ce da ta leqa kowane gida, idan babu ɗan gidanku akwai wani daga ahalinku ko maƙwafcinku, kuma babban abin damuwar shi ne idan kana tunanin naka ba ya ciki, to abu ne mai sauqi abokai su yaudare shi ya tsunduma, babu maganar shaye-shaye a loqo ko a kango, yanzu babu jami’a babu sakandare, ko ina za ka iya ganin matashi kamarka, kamata/kamarki a cikin wannan harka.

Idan har mu ka ce kullum sai dai mu ta magana akan siyasa, cin hanci ko tsokanar juna, to mu na gani al’ummar mu kullum za su yi ta faɗa wa cikin halaka, kuma muna da gudummawar da za mu bayar, amma mun yi ‘ƙemagadas, wai shi Bahaushe idan jifa ya wuce kansa kawai ya faɗa kan ko ma waye.

Idan har Gwamnatin na ƙoƙari wajen ganin ta daƙile safarar waɗannan miyagun ƙwayoyi, to dole ne su ma iyaye su sanya idanu akan ‘ya’yansu, dole ne iyaye susan abokanan ‘ya’yansu, susan da waɗanda ke mu’amula da su tare da da sanya idanu akan ɗakunan kwanansu, da yawansu sukan ƙunshe kansu a cikin ɗaki tare da fesa turare idan kayan mayen na hayaƙi ne, ko kuma su kulle ɗakin tare da amfani da kwalbar lemo don zuba kayan mayen a ciki, iyaye na can ɗaki basu san abin da ke faruwa ba, a haka yaran kullum ke girma cikin ɗabi’ar maye, daga nan kuma har tabi jikinsu, shi ke nan sai su ja ra’ayin abokanansu, a-haka-a-haka al’ummarmu kullum ke afka wa cikin bala’i da masifu, saboda saɓon Allah.

Ita kanta gwamnatin kawai damuwarta iyakokin ƙasarta, amma ta ɓarauniyar hanya wasu na shigo da waɗannan kaya, su raba su ga masu kantinan sayar da magunguna na unguwa, yayin da su kuma su ke dillancinsa ga yaranmu. Dole ne gwamnati ta sa ido akan masu ‘chemists’ na unguwanni, haka suma iyaye su bada haɗin kai wajen haɗa kwamitin unguwa, duk me ‘chemist’ ɗin da aka samu yana sayar da wannan kayan maye, to Gwamnati ta soke lasisinsa na sayar da magani.

Ita kanta hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi dole ne takara himma wajen sanya idanu akan masu sayar da magungunan, domin da yawansu suna da waɗanda suke sayarwa da waɗannan magungunan akan farashi mai tsada, dole ne hukumar farin kaya su yi amfani da kaifin basirarsu wajen cafke irin waɗannan ‘yan kasuwa da ake haɗa baki da su a na lalata al’ummarmu. Sannan akwai gurare waɗanda ya kamata Gwamnatin ta bada ikon shiga tare da damƙe masu wannan harka, da yawan ɗakunan kwana na baki (hotels), gidajen shaƙatawa tare da guraren wasanni duk wannan harka ta zama ruwan dare.

Wannan fa babban bala’i ne ga al’ummar mu da kuma addininmu wanda ya hana shan kayan maye, dole ne a kawar da wannan mummumar ɗabi’ar idan har muna son mu samar da al’umma ta gari, dole ne mu kawar da son rai, don ganin al’ummarmu ta na cigaba ta kowace fuska ta rayuwa.
Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad a Kaduna, 08168716583.

Naɗin sabon shugaban malamai a Jihar Kano

Mun ji cewa, sanarwa ta naɗa Sheikh Dakta Abdullahi Sale Pakistan a matsayin shugaba na majalisar malamai ta Jihar Kano, inda ya maye gurbin Sheikh Ibrahim Khalil, hakan ya tada wa wasu hankali sun ƙaryata cewa fau-fau-fau ba gaskiya ba ne.

Amma a yi ɗan nazari ba tare da saka siyasa ko wata ɓoyayyiyar manufa ba, don kada a janyo wa addini wata tangarɗa. Abun nufi shi ne, naɗin an ce ɓangarorin Izala da Ɗarikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya ne su ka haɗu.

A nan zan ce waɗanda ke nuna turjiya ra’ayinsu ne. Amma a yi taka-tsan-tsan ganin yadda matsaloli iri-iri ke addabar mu Musulmi, musamman waccan fitinar wacce ta kai an gurfanar da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara a kotu bisa wasu tuhume-tuhume masu muni a Musulumci, kuma sai a ji wasu na ƙoƙarin janyo wata husuma kawai, domin an saɓa wa tasu buƙatar.

Kanawa a kula! Musulunci addini ne wanda ke umurni da haɗin kai wajen gina juna ta fuskar ilimi da adalci. Allah ya kawo ma mu mafita da fahimtar juna.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519.

Zaɓen 2023

Ga dukkan alamu kudanci da arewaci na da mabambanta na fatan wanda zai maye gurbin shugaban ƙasa mai ragamar mulki a yanzu, Muhammadu Buhari. Kar mu manta cewa gwamnoni a kudanci sun fitar da aniyar gurin nasu ya mayi gurbin Shugaban ƙasa Buhari, inda a Arewa hatta ƙungiyar ACF ta nu na buƙatar a bar ma jama’a zaɓin su a zaɓen 2023 wanda hakan ke fiddo muddin ta kasance a hakan arewa ce mai alamun cigaba da riƙe ragamar tafiyar da ƙasar.

Sai dai wani lamari mai kama da badda bamu ko gogewar siyasa, wani fitaccen ɗan siyasa, Mr Raymond Dokpesi a wata tattaunawa da jaridar Daily Trust wacce ta fitar a makon jiya a shafi na (7), ɗan siyasa Mr R Dokpesi ya nuna zai yi wuya wani ɗan siyasa na kudanci ya samu nasara a zaven 2023.

Ko shakka babu magana ce wacce za ta ƙarfafa gwiwar ‘yan siyasa na arewa, amma ni a tawa shawarar mafita ita ce a samu wanda ke da kishi da amana da sauraren ƙorafin talakawa a duk matakai tun daga kansila har sama.

Daga Mukhtar Ibrahim saulawa Katsina, 07066434519, 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *