PDP Za Ta Amshi Mulki A 2023, Inji Saraki

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, ka tsohon gwamnan Kwara, Dr. Abubakar Bukola Saraki a shirye PDP ta ke ta ƙwace mulki a shekarar 2023.

Saraki ya faɗi haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi yau Talata da gidan talabijin na AriseTv.

Tsohon Shugaban Majalisar ta Dattawa ya bayyana cewa a yanayin yadda Nijeriya take a rarrabe, zai ba PDP dama ta lashe zaɓen 2023.

Ya ce, Nijeriya ba ta faɗa wa hali da yanayin rarraba ba irin na wannan lokaci a ƙarƙashin mulkin Buhari.

“Muna da duk wani abu da ake buƙata don a lashe zaɓe, saboda yanayin da ƙasar ta tsinci kanta a yanzu.

“Tun bayan yaƙin basasa, ba a taɓa samun rarrabuwar kawuna a Nijeriya ba irin yanzu. Ana fama da matsanancin rashin aikin yi, rashin tsaro, da sauransu. Kuma duk waɗannan abubuwan akwai alƙalumma da ke nuna haka. Ba wai ina magana ba ne a matsayin shugaba a tsagin adawa” inji shi.

Yayin da aka tambaye shi ko idan ya rasa tikitin takara zai sauya sheƙa zuwa APC. Saraki ya ce, babu wannan maganar.

“Kwanan nan wasu jiga-jigai daga APC za su bar jam’iyyar su dawo PDP”.