Ƙungiyar ta’addanci ta Lukarawa ta ɓullo – Hedikwatar Tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da aka fi sani da Lukarawa a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis a Abuja.

Janar Buba ya bayyana cewa, sabuwar ƙungiyar ta’addancin ta samo asali ne daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan, wanda ya kawo cikas ga haɗin gwiwar sojoji tsakanin Nijeriya da Nijar.

Ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun fara kutsa wa yankunan arewacin jihohin Sakkwato da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.

A cewarsa, ayyukan haɗin gwiwa da jami’an tsaron Nijar da aka yi a kan iyakokin ƙasar, da a baya kafin juyin mulkin, ya sa ‘yan ta’addan suka yi kaca-kaca da su.

Ya ce, “’Yan ta’addan sun yi amfani da giɓin da ke akwai na haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu, inda suka yi amfani da wurare masu wahala, inda suka kutsa wasu yankuna masu nisa a wasu jihohin Arewa maso Yamma domin yaɗa aƙidarsu.

“Da farko mutanen yankin sun yi maraba da ‘yan ta’addan da suka yi imanin cewa suna da kyakkyawar niyya. Sai dai ba a kai rahoton tafiyar ga sojoji da hukumomin tsaro ba.”

Kakakin Tsaron ya ba da tabbacin cewa sojojin sun ci gaba da ci gaba da kokarin leken asiri, sa ido da kuma bincike (ISR) don ƙasƙantar da ‘yan ta’adda.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar na ci gaba da amfani da manyan wuraren da ba na gwamnati ba domin ɓuya, gujewa sojoji, da kuma muzgunawa jama’ar yankin amma ya bayyana cewa dakarun na gano inda suke tare da kawar da wannan barazana.

Manhaja ta rawaito cewa, rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Sakkwato ta kuma tabbatar da kasancewar ƙungiyar a ƙananan hukumomi biyar na jihar.

Kakakin rundunar, Ahmed Rufa’i ne ya bayyana hakan ga wakilinmu a ranar Laraba.

Ya ruwaito cewa, ƙungiyar ɗauke da manyan makamai, tana gudanar da ayyukanta a Gudu, Tangaza, Binji, Illela, da kuma wata ƙaramar hukumar, inda take yaɗa manufarta.

By ukarofi