Ɗan sanda ya bindige abokin aikinsa a ƙoƙarin razana masu zanga-zanga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An tabbatar da mutuwar wani jami’in rundunar ’yan sandan Nijeriya tare da wasu mutane biyar da suka jikkata a wani rikici da ya varke a yayin aikin samar da zaman lafiya a kasuwar Jos da ke jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ’yan sanda, da ma’aikatan gwamnati, jami’an NSCDC, da jani’an hukumar shige da fice da Operation Rainbow da ke da alhakin tabbatar da tsafta a kasuwa, inda suka fuskanci turjiya mai tsanani daga jama’a.

A ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya wani jami’i ɗaya ya yi harbin gargaɗi amma abin takaici harsashin ya sami ɗan sandan wanda ya mutu nan take tare da jikkata mutane biyar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Filato, Mista Emmanuel Adesina ya ziyarci wurin domin duba halin da ake ciki, inda kuma aka nan take aka cafke jami’in da ya yi harbin domin gudanar da bincike.

Hukumomin ƙasar sun ce an ajiye gawar jami’in mamacin a ɗakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da bincike.

A halin da ake ciki, an dawo da zaman lafiya a yankin tare da jami’an tsaro a ƙasa domin ci gaba da aiwatar da dokar.