2023: An cafke shugabannin ƙananan hukumomi biyu da bindigogi a Kano

*’Yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An cafke wasu shugabannin ƙananan hukumomi guda biyu na Jihar Kano sakamakon zargin da ake yi na kama su bindigogi da aka yi a yayin gangamin siyasa jiya, Alhamis.

Bugu da ƙari, wasu ’ƴan daba da ake kyautata zaton ’ƴan bangar siyasa ne, sun farmaki magoya bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar adawa ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a Jihar Kano.

Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a unguwar Na’ibawa da ke kan titin zuwa Zariya.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, yayin farmakin, magoya bayan na kan hanyarsu ta zuwa garin Kwanar Ɗangora ne, domin tarbar ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jiya Alhamis yayin da aka kai musu harin.

Kazalika, an lalata aƙalla motoci 10 tare da ƙone wasu yayin farmakin.

Rundunar tsaro da haɗin gwiwa da ta haɗa da sojoji, ’ƴan sanda, SSS da NSCDC, sun kama shugabannin ƙananan hukumomin Ungogo da Rimin Gado na Jihar Kano, Abdullahi Ramat da Munir Ɗahiru, da bindigu.

Wata majiyar sirri ta jami’an tsaro ta shaida mana cewa, an kama mutanen biyu ne a lokacin da suke jagorantar ’ƴan daba, domin su kai farmaki kan ayarin motocin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a hanyar Zariya da ke Kano,

“Rundunar tsaron ta haɗin guiwa na tsaka da sintiri na tauna tsakuwa a lokacin da su ka ci karo da shugabannin da ke jagorantar ‘yan daba. Nan take jami’an tsaro su ka karɓe bindigogin daga hannun ciyamomin tare da cafke ‘yan baranda sama da 100 da suka yi wa dan takarar jam’iyyar NNPP kwanton vauna.

Majiyar ta ƙara da cewa, “a halin yanzu ana tsare da su a sashin binciken manyan laifuka, kuma jami’an tsaro na haɗin gwiwa na ci gaba da sintiri a cikin birnin domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin.”

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce, sun kama mutane da dama, kuma za su yi cikakken bayani bayan kammala bincike.

Harin dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da jam’iyyun da ‘yan takararsu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu a Abuja.

Wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, Tasiu Lawal, ya ce ya bi ta jikin wata babbar motar da yake ciki, ta hakane ya tsira.

“Na tsere da ƙyar. Alhamdulillah. Sai aka ce mana su (’yan baranda) suna nan suna jiranmu, sai muka tsaya a Na’ibawa muka tabbatar muna da yawa kafin mu ci gaba da tafiya.

“Ba tare da sanin kowa ba, suka zo ta kowane ɓangare suka far mana. Sun fara kai mana sara da addunan ciki har da mata rike da adduna,” inji shi.

Jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, an tura su wurin da lamarin ya faru.

Har ya zuwa lokacin da muke haɗa rahoton nan, ɗan takarar na Shugaban Ƙasa Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, bai iso cikin birnin Kano ba, sai dai akwai cincirindon jama’a da suka fito a bakin titi suna dakon sa tun daga kan shatale-talen Dangi zuwa zuwa gadar Naibawa.