Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Katsina, inda daga nan ne zai zarce zuwa Daura, mahaifarsa, domin halartar zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi gobe Asabar.
Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Umar Musa Yar’Adua da misalin ƙarfe 4:40 na yammacin jiya Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023.

A gobe Asabar ne ake sa ran zai kaɗa ƙuri’arsa ga ‘yan takarar da yake so a Daura.

Kafin ya bar Abuja zuwa Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Buhari ya kira taron majalisar tsaro, inda ya gana da shugabannin hukumomin tsaro domin tunkarar su kan batun kare masu zaɓe da kuma tabbatar da cewa zaɓen ya gudana.

Buhari ya kuma gana da Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a Abuja, Babban Birnin Tarayya, inda ya gargaɗe shi da ya tabbatar an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.