Yadda gwamnonin Nijeriya suka butulce wa Shugaba Buhari bayan ya fitar da su kunya

Daga BASHIR AHMAD

Yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ceto gwamnonin Nijeriya daga halin ni-`ya-su na matsin tattalin arziki a yayin da jihohinsu suka shaƙi ƙamshin mutuwa ta hanyar bijiro da tallafin Gwamnatin tarayya ba voyayyen abu ba ne a ƙasar nan, kowa ya sani.

Shakka babu jama’a na ankare da yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, ta samu Nijeriya a cikin wani mayuwacin hali a shekarar 2015, baya ga fama da matsaloli masu nasaba da rashin tsaro da ayyukan tayar da ƙayar baya na Boko Haram, akwai kuma matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da suka tilasta wa ƙasar tsayawa cak a wancan lokaci. Wanda hakan ya sanya tunani a zukatun wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke ciki da wajen ƙasar nan tare da amanna da cewa ban da zuwan Buhari, da irin kishin ƙudirinsa na alkhairi da yake da shi ga ƙasar, da tuni magana ake ta yadda ƙasar ta tsinci kanta cikin yanayi na tsananin rikicin da zai sa ta zama labari.

Tsananin da ya sanya masu ƙaramin ƙarfin har ma da masu hanu da shuni cikin wani yanayi na ƙunci a wasu daga cikin jihohin da ke faɗin ƙasar nan ko da kuwa ba a ce dukkansu ba, tsananin matsin tattalin arzikin da aka tsinci kai a ciki ya sanya wasu daga cikin gwamnonin ƙasar nan kasa biyan albashin ma’aikata a jihohinsu tare da ciyo bashi daga wasu wuraren, baya ga irin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya take turo wa jihohin domin yin wasu ayyuka da biyan albashi da ya zamana tilas a wuyan gwamnati.

Hakan dai ya bayu ne zuwa wani yanayi da gwamnonin ke fakewa a bayansa na ƙarancin kuɗaɗe da rashin samar da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’ummar da suke shugabanta.

To, sai dai a iya cewa zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa, ya yi tasiri ƙwarai da gaske wajen ceto waɗannan jihohi daga halin ƙamshin mutuwar da suka shaƙa ta hanyar karvar tallafi daga gwamnatin Buhari, ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ba.

Tallafin kuɗaɗen ‘Bailout’, Paris Club har ma da na Cutar Korona (COVID-19).

Tallafin Kuɗi Na ‘Bailout’
Tun bayan rantsar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bijiro da tsarin bayar da tallafin kuɗi na ceto jihohi daga ƙaƙa-ni-ka-yi da ake kira da ‘Bailout’, inda aka fitar da tsabar kuɗi har Naira Biliyan 477 domin farfaɗowa tare da inganta rayuwar wasu daga cikin jihohin Nijeriya, qari da wasu kuɗaɗen da gwamnonin jam’iyyar APC suka nema na ƙarashen kuɗaɗen ayyukan manyan titunan da suka ƙarasa mallakin gwamnatin tarayya a jihohinsu.

Wanda bincike ya gano cewa ba wannanne karon farko da gwamnonin ke neman kuɗi da nufin ƙarasa ayyukan gwamnatin tarayya ba, inda ko a gwamnatocin baya an samu irin wannan iƙirarin daga wajen gwamnonin.

Sai dai ba wai iya tallafin kuɗin biyan albashi gwamnatin Buhari ta agaza wa da gwamnonin ba har da kuɗaɗen da za su biya Ariyas ga ma’aikata.

Tallafin Paris Club

A magana ta gaskiya da zahirin abin da ya bayyana a lokacin da jihohi suka tsinci kansu a halin ƙamfar kuɗi da rashin fara gudanar da ayyukan raya ƙasa da walwalar al’umma, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bai wa gwamnatin tarayya umarni da a bai wa dukkanin wata jiha zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 10 na tsawon watanni 8, a dai dai lokacin da farashin gangar ɗanyen man fetur ya faɗi a kasuwar duniya.

Idan `yan Nijeriya za su iya tunawa an yi wani lokaci da jihohi ke kokawa kan rashin amfana da bashin Paris Club, wanda hakan ya tilasta wa gwamnatin tarayya ware musu nasu kason. Mun kuma san cewa ban da jin ƙai irin na Shugaba Buhari da wasu gwamnonin da jihohinsu babu inda za su je.
 
Tallafin Korona (COVID-19) Ga Jihohi

A shekarun baya, a daidai lokacin da ƙasar nan ta shiga wani yanayi na halin matsin tattalin arziki sakamakon vullar cutar Korona (COVID-19) wanda ba wai Nijeriya lamarin ya shafa ba kaɗai, a’a duniya ce baki ɗaya, amma cikin adalcinsa, Shugaba Buhari ya ɓullo da wasu hanyoyin tallafa wa gwamnoni da nufin tallafa wa talakawan da ke zaune a gida, wanda har aka zargi wasu daga cikin gwamnonin da karkatar da kayan tallafin domin amfanin kansu, wasu kuwa ajiye kayan suka yi har sai da ruwa ya lalata su aka yi ba-wan-ba-ƙanin.

Mu Kalli Wani Abu ta Mahangar Siyasa

Idan muka ajiye maganar ceton jihohi da gwamnoni da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta yi a ƙasar nan ta hanyar tallafa musu ta hanyoyi daban-daban, na tabbatar da cewa `yan Nijeriya sun aminta da cewa wasu daga cikin gwamnonin musamman na jam’iyar APC sun shiga rigar mutunci da alfarmar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ta silar haka suka lashe zaɓukansu a jihohinsu, na san ba za a taɓa mantawa da abin da aka yi wa take da “Guguwar Buhari” ba.

To, amma abin takaici shi ne yadda wasu daga cikin su har yanzu jahilci ya hana su fahimtar ba domin shi ba da tuni da dama daga cikinsu na gidan Yari, wasu kuwa suna can an manta da babinsu a duniya.

Haka kuma shugaban ya tsaya kai da fata wajen ƙarfafawa talakawan ƙasar nan ƙwarin gwiwar zaɓensu domin ba su dama su jagorance su tare da tunanin cewa su ma suna ƙaunarsa tsakani da Allah, wanda a zahiri Musa ne a baki Fir’auna a zuciya, wasu kuwa ravuwa suke da hotunansa a yayin gangamin yaƙin neman zavensu domin kuwa sun yarda da cewa Buhari, ya zo da manufofin da za su ceto wannan qasa daga halin da ta tsinci kanta a wancan lokaci.

To, sai dai cikin mamaki wai a ce waɗannan gwamnonin da suka shiga rigar alfarmar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ne a gaba-gaba wajen cin amanarsa da faɗa masa maganganun da ko ƙuda ba zai kalla ba ballantana ya ci, kuma ba don komai ba, sai don yinƙurin shugaban ƙasan wajen tabbatar da cewa an samar da sahihin zaɓe ga `yan ƙasa da za su aminta da shi.  Ashe ba a banza ba masu zalaƙar iya harshe ke faɗar “siyasa ba ta da gwani”.

 Me Ya Kamata `Yan Nijeriya Su Sani?

Ya kamata al’umma su sani cewa tsarin sauya fasalin takardun kuɗi da gwamnati ta bijiro da shi an yi shi ne da kyakkyawan qudiri domin ci gaban Nijeriya da kuma samar wa da ƙasar kyakkyawar gobe.

Haka kuma ƙudirin da ake sa ran zai daƙile matsalolin cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziƙin ƙasa har ma da sauran wasu abubuwan da ka iya kawo naƙasu ga ci gaban wannan ƙasa.

Baya ga wannan halin matsi da wannan doka ta zo da ita wanda masana da dama suka yi amanna gaba za ta yi kyau, ya kamata `yan Nijeriya, su sani cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ba mai satar kuɗin ƙasa ba ne, haka kuma ba mayaudari ba ne, hasalima ba zai tava yin abin da zai sanya rayukan talakawa cikin hatsari ba.

Har ila yau, ya kamata mu tambayi kanmu, me ya sa gwamnonin suke ƙalubalantarsa kan wannan doka? Me ya sa ba su yi haka a kan sauran ƙudirorin da suka shafi talaka kai tsaye ba? Me ya sa ba su ƙalubalanci wasu dokokin da aka yi a baya ba wanda wasu ma ba su da masaniyar yin su, amma me ya sa sai wannan?

A ƙarshe zan ƙarƙare da ba da shawarar cewa, idan har yanzu kana ko kina ajiye da tsoffin takarardun kuɗi to, a yi ƙoƙari a kai su Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin a canza su, duk yawansu, matuƙar ka kasan halak malak ɗinka ne, domin ciki da gaskiya, wuƙa ba ta huda shi…

Bashir Ahmad shine Mai Taimaka Wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na Musamman A Kan Shafukan Sadarwa na Zamani