2023: Mulkin Buhari ba komai ba ne face yaudara, inji Saraki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce jam’iyya ce mai cike da yaudara da mayaudara.

Saraki ya bayyana hakan ne a Bauchi, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, lokacin da kwamitin yaƙin neman zaɓensa ya ziyarci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP domin neman shawari a sakateriyar jam’iyyar a Bauchi.

Saraki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2023, Farfesa Tyorwuese Hagher, ya ce APC ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka wa ‘yan Nijeriya a yaƙin neman zaven 2015.

“Shekaru bakwai a jere, har yanzu suna ganin laifin PDP amma duk da haka, ba za su iya zama daidaita ci gaban da PDP ta kawo ba.”

Ɗan siyasar na Nijeriya ya kuma ce jam’iyyar ta lalata lamurra a Nijeriya.

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya buƙaci ‘yan Nijeriya da kada su kula da inda ya fito da kuma addinin da yake bi, kawai su zaɓe shi shugaban ƙasa bisa cancantarsa kamar yadda ya ce ƙasar na buƙatar shugaban da zai iya haɗa kan ƙasar nan da kuma dawo da zaman lafiya.

Saraki ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su zaɓi shugaban da zai sake dawo da martabar jami’o’in ƙasar nan, wanda zai samar da man fetur da kuma tabbatar da inganta wutar lantarki domin inganta tattalin arziki.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawan tarayya, Bukola Saraki, ya lashi takobin naɗa matasa masu shekaru ƙasa da 35 idan ‘yan Nijeriya suka zaɓe shi matsayin shugaban ƙasa a 2023.

Saraki wanda ya mulki jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011 ya yi wannan alƙawari ne ranar Talata, 22 ga watan Maris a shafinsa na Tuwita, inda ya ce, “zan yi aiki fiye da yadda na yi niyya. Ina alƙawarin cika burikan dukkan matasanmu.”