2023: Zan kasance ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, inji Atiku

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Yayin da shirye-shiryen zaɓen shekara ta 2023 suka fara kankama, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Asabar da ta gabata ya ziyarci ubangidansa, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kuma fitaccen basarake na ƙasar Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo.

Atiku, wanda ya isa gidan Olusegun Obasanjo da misalin ƙarfe 10 na safiyar wancan rana, sun yi ganawar ta sirri na kimanin  awa guda.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan ganawar tasu, Atiku ya ce, “na zo ganin ubangidana ne” amma bai ce komai akan lamarin da suka tattauna ba a lokacin ganawar.

Ya yi kira ga matasa ‘yan Nijeriya da su kasance masu yin gasa da dattijai bisa takarar muqamai a zavuvvukan shekara ta 2023, har ma da ta kujerar shugabancin ƙasa, yana cewar, ba daidai ba ne a takewa dattijai ‘yancin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya basu na neman cimma burace-buracen su na siyasa.

Atiku, wanda shine ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a shekarar zaɓe ta 2019, ya bayyana cewar, fagen takarar siyasa a buɗe yake ga kowa da kowa, har da matasa, yana mai nuna ƙwarin guiwar kasancewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar tasu ta PDP a shekarar zaɓe ta 2023.

Ya ce, shine mafi cancanta da zama shugaban ƙasar nan a shekara ta 2023 da zai fito da Nijeriya daga ƙangogin da suka addabe ta.

 “Na zo na ga ubangidana ne, za mu sanar da ku idan na ayyana aniya ta, za mu bayar da sanarwa a siffance’. Ba ri mu gani yadda matasa za su buga da dattawa.

“Na taɓa rasa tutar tsayawa shugabancin ƙasa ne? Gasa ce, kuma dimokraɗiyya kenan,” a cewar Atiku.
Atiku daga bisani ya zarce zuwa Fadar Alake na Ƙasar Egba (Egbaland), Oba Adedotun Gbadebo, a Ake ta cikin Abeokuta, inda ya yi ta tuna lamura da suka inganta dangantakar sa da mutanen jihar Ogun, musamman ma mutanen ‘Egbaland’.

Ya yi tuni da cewar, ya fara sana’a ko hidimar aikin kostom ne ta hukumar hana fasa ƙwabri a jihar Ogun, kuma a nan ne Allah ya albarka ce shi da fara auren mace.

Ya bayyana cewar, Jihar Ogun tamkar gida ne a gare shi, yana mai bayar da tabbacin zai cigaba da alaqanta kansa da jama’ar jihar Ogun, musamman ma na garin Abeokuta.

Duk da cewar, Atiku bai bayyana wata manufar sa ta siyasa ba a fadar sarkin, Basaraken ya yi addu’ar Allah ya sa ya cimma buƙatun sa.