Wai me maza suke so wajen mata?

Daga AMINA YUSUF ALI

Tambayar wai me maza suke so wajen mata? Wannan tambaya ce mai cike da sarqaqiya wacce da wuya ta iya amsuwa kai tsaye. Domin yadda mata suka banbanta a ra’ayi, haka mazan ma suka banbanta domin banbancin ‘yan adamtaka. Kodayake, dukkan maza sukan haɗu a kan wasu abubuwa da ake ganin kowannensu yana buƙata daga mace. Mata sun sha yin kuskuren namiji yana buƙatar kyawu ko surar halittar mace ne fiye da komai. Shi ya sa suka fi mayar da hankali wajen yi wa kansu kwaskwarima da gyara domin samun waccan soyayyar ta ɗa namiji. Sai dai abinda ba a fahimta ba, kashi ma fi ƙanƙanta ne sosai na maza suka fi fifita halittar mace a kan sauran abubuwan da mata suka tara. Eh da gaske halitta da surar mace ita ce abu na farko da yake fara jan hankalin namiji gare ta, a ma fi yawancin lokuta. Amma daga tafiya ta yi nisa, wancan son da sha’awar sai su kasa riƙe auren ko alaƙar soyayyar. Ga wasu abubuwan da bincike ya nuna cewa maza da yawa sun fi so wajen mata:

 1. So: kowanne namiji yana buƙatar soyayya a wajen mace. Yadda zai samu ƙwarin gwiwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa. Idan ya tuna akwai wacce take sonsa tsakani da Allah a rayuwa. Mace idan tana son namiji za ta yi haƙuri da duk naqasunsa kuma ta jiɓanci lamurransa, sannan za ta yi masa biyayya. Kuma za a samu zama na fahimtar juna.
 2. Nutsuwa da sirri: Namiji yana buƙatar macen da za ta sa masa nutsuwa kuma ta saurare shi a duk lokacin da ya zo mata da kokensa. Ko da ba ta ba shi shawara ba, a ƙalla ta saurare shi ba tare da rarraba hankalinta tsakanin saurarensa da yin wasu abubuwan ba. Kuma duk abinda ya tattauna da ita ya zama sirrinta wanda ba za ta iya shelanta shi ga wasu ba.
 3. Girmamawa: Kowanne namiji yana buƙatar girmamawa daga mace. Wato dai ta dinga kallonsa a matsayin shi ne jagoranta wanda ya isa da ita. Sannan ta zama mai masa biyayya a kan abinda ya yi umarni da abinda ya hana.
 4. Sarari: Namiji yana buƙatar mace wacce ba za ta zama mai nanuƙarsa koyaushe ba. Wacce za ta dinga ɗan ba shi sarari a koyaushe yadda zai dinga numfasawa ya samu ya yi al’amuransa. Tare da ƙarfafa masa gwiwa ba tsangwama, idan yana gudanar da abubuwansa.
 5. Amana: Yana buƙatar mace mai amana kuma wacce za ta amince masa shi ma. Wacce za ta sakankance da shi. Yadda idan ya ba ta amana ba zai ji ɗar ba, to ita ma yana buƙatar ya ga haka daga gare ta. Wacce ba za ta zarge shi ba kuma ba za ta guje shi ba a kan dukkan abinda ta faru a rayuwa ba. Kuma ta riƙe amanar kanta da kanta ba za ta kula kowa ba sai shi.
 6. Mara ƙarya da almundahana: Kowanne namiji yana buƙatar mace wacce take gaskiya da gaskiya ba almundahana ko cuta a ranta. Kuma ba ta yi masa ƙaryar asali ko wani abin ba.
 7. Gamsuwa: Kowanne namiji yana buƙatar wacce za ta gamsar da shi a fannin auratayya. Kuma ita ma ta zama mai mararinsa ba tare da shamaki ba ko kyararsa ba.
 8. Kulawa: Kowanne namiji yana buƙatar mace wacce zai dinga samun kulawa daga gare ta. Da tausayawa da tausasawa. Wacce za ta dinga nuna ƙarara ta damu da shi.
 9. Kyautawa: Maza na son mace mai ƙoƙartawa wajen son faranta musu rai. Musamman idan suka shiga wani ƙunci na rayuwa da suke buƙatar a tallafa musu. Amma fa su ma mazan su sani, kyautatawar tana biyo bayan su ma kyautayawar da suka nuna mata. Wato ban gishiri in ba ka manda.
 10. Ganin girman iyayensa da dangi: Duk son da namiji yake yi wa mace, har abada danginsa da iyayensa suna samanta a zuciyarsa. Don haka, kowanne namiji ya fi son ya samu matar da za ta taya shi riƙewa da ƙaunar danginsa yadda ya kamata. Don haka, yana gudun mai wulaƙanta haularsa.
 11. Tausayawa: Namiji yana buƙatar tausayawar matarsa wacce idan yana cikin wani hali za ta zama mai rarrashinsa da ban-baki.
 12. Tsayayya: Kowanne namiji yana son mace tsayayya wacce ba ya shakku a kanta idan ya ba ta al’amuransa za ta tafi da su kamar yana nan. Idan namiji yana da irin wannan matar, ba ya wani ɗar ko fargaba. Kuma wacce idan yana buƙatar wani abu wajenta, zai je kai-tsaye don ba shi da shakku a kanta.
 13. Tarbiyya da asali: Namiji na son tarbiyya a wajen mace. Domin yana sa ran idan suka samu zuriyya, za su samu tarbiyya ta gari. Haka namiji na son mace mai asali wacce ba zai yi fargabar haɗa tsatso da danginta ba.

14: Basira da ƙwaƙwalwa: Namiji na son mace mai basira da ƙwaƙwalwa wacce za ta dinga yi masa tunani me kyau. Ko matsala ya kawo mata, za ta iya ba shi shawara da samar masa da mafita.

Waɗannan su ne wasu daga abubuwan da bincike ya nuna maza suna so a wajen mata.
Amma zancen a faɗi ainahin kowanne namiji me yake so wajen mace, tambayar ba za ta taɓa amsuwa ba. Saboda abincin wani gubar wani ne. Kowa da zaɓinsa. Macen da kake gani ba ta ishe ka kallo ba, a wajen wani namijin fa ita ce ƙarshen burinsa. Domin amsa tambayar sai dai a yi nazarin halayya ta kowanne namiji ko mace don gano ainahin mai suka fi so a juna.

Don haka, mata su daina wahalar da kansu wajen canza kansu da tilasta kansu sai sun yi koyi da wata da suka ga ana so. Ke ma ki haƙura da Allah ya yi ki. Domin wani yana nan ke kuma sak irinki haka yake son mace. A Duniyar nan ba shi da zaɓi sai ke.

A ƙarshe, ina fatan alkhairi ga masu karatu. Da fatan za ku cigaba da bibiyar filin Zamantakewa na jaridarku mai farinjini ta Blueprint Manhaja. Mu haɗu a wani makon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *