2027: IGP Disu ya yi alƙawarin ’yan Nijeriya za su yi alfahari da ’yan sanda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa yadda jami’an ’yan sanda za su gudanar da ayyukansu kafin zaɓen 2027, lokacin zaɓen da kuma bayan kammala shi, zai sa al’umma su yi alfahari da rundunar ’yan sandan ƙasar.

Disu ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin ’yan jarida bayan ƙaddamar da wani littafi mai suna The Origin of Women in Nigeria Police Force, wanda Dame Stella Okuyiga, mai shekara 96 kuma tsohuwar Mataimakiyar Kwamishinan ’Yan Sanda mai ritaya, ta rubuta.

Okuyiga na cikin mata 20 na farko da suka shiga aikin ’yan sanda a Nijeriya a shekarar 1955.

Da yake magana kan shirye-shiryen rundunar ’yan sanda gabanin babban zaɓen 2027, IGP Disu ya ce rundunar ta gudanar da taro da kwamishinonin ’yan sanda daga sassa daban-daban na ƙasar da sauran manyan jami’ai domin tabbatar da ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki yayin zaɓen mai zuwa.

Ya ce rundunar ta yi nazari kan yadda jami’anta suka gudanar da ayyukansu a zaɓukan da suka gabata, inda ta yi la’akari da abubuwan da suka yi nasara da kuma wuraren da aka samu gazawa, domin inganta ayyukanta a zaɓen 2027.

“Na ba ku tabbaci cewa ’Yan Sandan Nijeriya za su yi aiki yadda ya kamata, kuma za mu sa rundunar ’yan sandan ta yi alfahari da kanta, sannan mu sa ’yan Nijeriya su yi alfahari da mu,” inji shi.

Da yake tsokaci kan littafin Okuyiga, Disu ya ce rundunar tana farin ciki da nasarorin da tsohuwar jami’ar ta samu, musamman yadda ta ɗauki lokaci ta rubuta tarihin rayuwarta da gogewarta a aikin ’yan sanda domin amfanin al’ummomin da za su zo nan gaba.

Ya ce rubuta tarihin irin waɗannan jami’ai zai taimaka wajen adana muhimman bayanai game da tarihin rundunar, tare da samar wa sabbin jami’an ’yan sanda, musamman mata, abin koyi da za su koya daga gare shi.

“Mama tana da shekara 96, kuma ta ɗauki lokaci ta rubuta dukkan gogewarta da ilimin da ta samu a aikinta, domin mu yi nazari a kansu, kuma matasan jami’an ’yan sanda mata masu zuwa su samu abin koyi,” inji Disu.

Ya ƙara da cewa rundunar tana fara wani sabon tsari na girmama waɗanda suka yi mata hidima, maimakon barin nasarorinsu su shuɗe ba tare da an adana tarihinsu ba.

“Mu a rundunar ’yan sanda, muna fara kafa al’adar da ba za mu manta da namu ba, ko mu bar gudummawar da suka bayar ta salwanta,” in ji shi.

IGP Disu ya kuma bayyana cewa rundunar za ta tabbatar da cewa an samar da kwafin littafin a dukkan makarantun horas da jami’an ’yan sanda na ƙasar, domin jami’ai su samu damar karanta shi tare da koyon darussa daga gogewar waɗanda suka gabace su.

Da take jawabi a wajen taron, Okuyiga ta bayyana farin cikinta da ƙaddamar da littafin, tana mai cewa wallafar za ta taimaka wajen tabbatar da cewa tarihinta da gudummawar da ta bayar za su ci gaba da kasancewa a rubuce, har bayan rayuwarta.

Ta ce, “Wannan ƙaddamar da littafi rana ce mai muhimmanci a rayuwata. Littafin zai kasance a nan, kuma ni ma zan ci gaba da rayuwa ta hanyar tarihin da na rubuta, domin za a ajiye shi a ɗakunan karatu a sassa daban-daban na duniya, mutane kuma za su ci gaba da karanta shi.”

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, wanda Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Dagogo Wokama, ya wakilta, ne ya ƙaddamar da littafin, inda ya bayar da gudummawar naira miliyan 20.

By ukarofi