Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
Wani malamin addinin Musulunci kuma shugaban makarantar AƙSAT ta Gombe, Dakta Auwal Abdullahi, wanda aka fi sani da Gafakan Akko, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga ƙoƙarin da jam’iyyun adawa ke yi na haɗa ƙarfi da ƙarfinsu domin kawar da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027.
A cikin wata hira da ya yi da manema labarai a Gombe, Dakta Auwal ya bayyana damuwarsa matuƙa kan yadda halin tsaro da tattalin arzikin ƙasa ke kara tabarbarewa a ƙarƙashin gwamnatin APC.
Ya ce wahalar da ‘yan Nijeriya ke ciki a yau ta kai matakin da bai taɓa kasancewa haka ba a tarihi.
“Yan Nijeriya na cikin wani hali na kunci da tsananin wahala yunwa, rashin aikin yi da tsadar rayuwa sun yi ƙamari fiye da yadda ake zato,” in ji shi.
Malamin ya jinjina wa gamayyar jam’iyyun adawa, inda ya yaba da rawar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ke takawa, yana mai cewa jam’iyyar na da hangen nesa, ƙwarewa da ƙarfin da za su iya dawo da ƙasar daga halin da take ciki.
“Wannan ba siyasa ce kawai ba halin da rayuwar al’umma Ke ciki za’a duba kuna Lokacin ceto ƙasar ya yi.
Ya ce Dole ne mu tashi tsaye, mu hada kai da addu’a da kuma ɗaukar matakin da ya dace tun kafin 2027,” inji Dakta Auwal.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su watsar da bambance-bambancen addini, kabila da jam’iyya, domin matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba su da bambanci suna shafan kowa da kowa ne.
Wannan kiran na Gafakan Akko na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ƙara ƙaimi wajen gina wata babbar gamayya da za ta iya fuskantar APC a 2027, domin kawo sauyi da dawo da bege ga talakawan Nijeriya.
