Ga dukkan alamu a tsakanin jam’iyya mai mulki APC da kuma waɗanda suka haɗu su kai ma ADC caffa su na da muradin ganin kowanne ɓangare ya amshi ragamar mulkin wannan ƙasar tamu Nijeriya a shekara ta 2027.
Allah ne masanin gaibu, amma dai za a kai ruwa a rana a kowanne ɓangare imma dai jam’iyya mai mulki ta yi tazarce ko kuma abin da ya wanzu a zaɓen 2015 ya sake maimaituwa.
Sai dai mu kula da kyau? Kwace wa APC mulki abu ne mai kamar da wahala ganin yadda talakawa sukai mwa APC ruwan ƙuri’u a shekara ta 2015 a bisa tsammanin za a samu komai a sauƙaƙe a mulkin Buhari amma a ƙarshe aka samu akasi. Hakan ya sanyaya gwiwar da dama wasu na ganin zaɓe na neman sauyi ya kau.
A gefe guda, tun yanzu masu lura da yanayi na siyasar ƙasarmu sun fara tsammanin wannan gamayyar na masu nemn kwace goriba a hannun ƙuturu sun makaro ganin da dama wasunsu da su akai waccen tafiya ta guguwar Buhari amma aka gaza raɓe Mushen tumkiya da yankaken kare ga halacci. wato a kai sauyi ya zamo kawai a tsakanin su yan siyasai. Don haka ni shawara ta ga ’yan uwana talakawa ita ce duk wata tada jijiyar wuya a tsakanin magoya baya a aje ta duk inda mutun ya nutsu ya tsaya amma ce ce kuce a daina addu’a ta neman zaɓin Allah ita ce mafita ganin su da dama bakinsu guda kuma muradun kai ne ya fi yawa a madadin kishin talaka.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519 / 08080140820.
