Assalamu alaikum, da fatan mun yi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.
Akwai wani abinda ke faruwa a ƙasar nan, mutane suna gwama lamarin siyasa da addini. Suna kamfen da sunan da sunan addini, wuce wani musulmi, wane ba Musulmi ba. Wasu har ɗaukar siyasa suke a matsayin jihadi.
Da masu addini Kirista da Musulmai za su gane, da kuma ’yan ƙabilanci za su gane, da basu riƙa damuwa da wannan siyasa ba. Domin addini daban siyasa daban, musamman ma a ƙasar Nijeriya.
Idan Addini ka ke so, ka koma gefe, domin babu ruwan Siyasa da Addini, idan kuma siyasa ka ke so to ka bar maganan addini. Ka yi siyasa, idan ka gama ka dawo addini. Kar ka ce zaka zaɓi wane saboda addini, ko za ka ki shi saboda addini. Addini daban Kuma siyasa daban.
Idan addini ɗaya ne ya ke da siyasa, gaya min wane jam’iyya Sahabbai su ke goyon bayan shi? Ko wane jam’iya Yesu Almasih yana tare da su?
ƙabilanci, wahala kawai ku ke sha, Na’am, dama dama ƙabilanci za a iya cewa tana da ɗan alaƙa da siyasa, amman ban da Nijeriya. Domin duk wanda ya ke yin siyasa saboda ƙabilanci a Nijeriya yana cikin wahala.
Iya abinda ya faru a zaɓi kan fidda gwani na jam’iyya da suka yi ya isa ga mai hankali ya fahimci wannan tafiya.
1. Kasheem Shateema, Tsohon Gwamnan Borno ne, Musulmi ne, Kuma ɗan Arewa ne, amman ya goyi Bayan Tinubu ɗan Kudu. ƙaddara duk da cewa Tinubu musulmi ne, amman ai ba ɗan arewa bane.
2. Orji Kalu, Kisista ne kuma gogaggen ɗan siyasa ne, kuma ɗan kudu ne, amman ya goyi bayan ɗan Arewa Musulmi Ahmed Lawal, me ya sa hakan ya faru, shin lokacin babu ɗan kudu ne a masu takarar?
3. Sanata Ali Ndume da Yusuf Burutai, Musulmai ne, kuma ’yan Arewa, amman sun goyi bayan ɗan kudu, kuma Kirista Ameachi.
4. Femi Fani Kayode, ɗan kudu ne, Kirista ne, gogaggen ɗan siyasa ne amman kuma ya goyi bayan ɗan Arewa, Musulmi, Yahaya Bello.
5. Kabiru Gaya, Musulmi kuma ɗan arewa ne, ya goyi bayan Osinbajo, kuma Pasto ɗan kudu.
Ya kai mai hankali, ka yi tunani ka gani, shin idan ka zage da sunan cewa kana son wani saboda addini ko ƙabikanci, to wallahi kana ruwa.
Kowanne ’yan siyasan mu, aljihun su suke gyarawa, fatan kowa miyarsa ta yi kyau to mene ne na ɓata lokacin ka da cewa sai wane Musulmi zan zaɓa bayan kuma kasan ƙasar ba ƙasar Musulunci ba?
Haka kaima Kirista, kar ka shiga siyasa saboda addini, domin ƙasar ba ƙasar Kiristanci ba ne. Kasa ce ta Dimukraɗiyya, ƙasa ce ta kowa da kowa, idan Addini ka ke so to ka bar siyasa ka koma addini, idan kuma siyasa ka ke kar kace kana addini.
Idan an kashe ka a siyasa, kar ka yi zaton saboda addini aka kashe ka. Idan ka yi jihadi a siyasa, fasadi ka yi ba jihadi ba. Jihadi yana addini, fasadi yana siyasa.
Allah ka bamu shugaba na gari, tare da kuma kawo ƙarshen ƙabilanci da ke tsaƙaninmu ’yan Nijeriya. Ameen
Saƙo daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].
