
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban hafsan tsaron dakarun Chadi a Maiduguri, Mista Bisso Youssouf Mbodou Mbami ya yi kira da a ƙarfafa haɗakar tsaro tsakanin Nijeriya da Chadi domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
Mista Bisso ya yi wannan kira ne yayin da ya jagoranci wata tawagar ofishin tsaron ƙasarsu a wata ziyara a hedikwatar jami’an haɗaka (JTF) na yankin Arewa ta Gabas da na atisayen Haɗin Kai (OPHK) a Maiduguri.
Ya ce, bunƙasa haɗaka tsakanin ɓangarorin ƙasashen biyu abu ne mai muhimmanci wajen cin galaba akan mayaƙan Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke haddasa matsi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa sadaukarwarsu wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa haɗakar dakarun ƙasashen biyu tsari ne da zai kai su ga nasara a shiyyar.
Kazalika, hafasan ya ce tattaunawa akan matsalolin iyakoki da kasuwanci zai taimaka wajen rage ratar sadarwa tsakanin garuruwa, inda ya ƙara da cewa gwamnatin Chadi tana aiki tuƙuru wajen wayar da kan ƴaƴanta akan tsare-tsare da dokokin kasuwancin Nijeriya.
A nasa jawabin, Kwamandan rukunin, Manjo Janar Abdulsalm Abubakar ya bayyana Chadi a matsayin abokiyar tafiya ga Nijeriya wajen tafiyar da lamuran tsaro da al’adu.







