
Majalisar Dattawa ta ce wajibi ne Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya mayar da kuɗaɗen da ba a bayyana yadda aka yi da su ba, waɗanda suka kai jimillar Naira tiriliyan 210 zuwa asusun tarayya.
Kwamitin Majalisar Dattawa akan ƙididdige adadin kuɗaɗen gwamnati ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada ne ya yanke wannan hukunci, bayan shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ya gaza bayyana a zaman kwamitin domin ya fayyace amsoshin tambayoyi da aka aika masa.
A binciken da aka gudanar kan ayyukan NNPCL daga shekara ta 2017 zuwa 2023, kwamitin ya gano cewa kuɗaɗe da ba a iya bayyana yadda aka yi da su ba sun kai tiriliyan N103 a matsayin kuɗin kashewa da kuma tiriliyan N107 a matsayin abin da ake bin kamfanin bashi.
Sanata Wadada ya ce, bayanan da kamfanin ya bayar suna cike da saɓani da rashin daidaito.
A watannin da suka gabata ne kwamitin ya gano wasu kurai-kurai a yadda kamfanin ya tafiyar da ayyukansa tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023, lamarin da ya tada bincike akan al’amarin.
