Remi Tinubu ta raba kayan tsaftar jinin al’ada ga ɗalibai mata a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta raba kayan tsaftar jinin al’ada ga ɗalibai mata a makarantun sakandare don inganta lafiyar su.

Sanata Oluremi Tinubu wadda matar gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta wakilta, ta bayyana cewar, a ƙarƙashin wannan shiri, za a rarraba kayan tsaftar jinin al’ada ga ‘yan mata 370,000 a faɗin ƙasar nan.

Hakazalika ta bayyana cewar, kowace jiha da babban birnin tarayya za su samu kunshi 10,000 na kayan tsafta.

A cewar ta, wannan taimako ne musamman ga ‘yan mata na ƙauyukka da ba su da ƙarfin sayen kayan tsaftar jinin al’ada.

“A yau, a nan jihar Zamfara, zan miƙa ƙunshi 10,000 na kayan tsafta domin rabawa ‘yan mata 10,000, yayin da kowacce yarinya za ta sami abin amfani da zai isheta har shekara guda”. Sanata Oluremi Tinubu ta ƙara da cewa

Mun zaɓi kayan tsaftar jinin al’adar ne saboda tsaftar su, sauƙin amfani, da kuma kariya ga lafiyar macce.

Tace shirin Renewed Hope Initiative (RHI), Ofishin ta yana da yaƙinin cewa ba za a taɓa barin yarinya ta rasa ilimin ta da mutuncinta ba.

Tayi Kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su ɗauki nauyin tabbatar da cewa kayan sun isa ga ‘yan mata na ƙauyukka kai tsaye, ba tare da an sayar da su ba.

Madam Tinubu ta ƙara da cewa, a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative, an kashe fiye da Naira biliyan biyu wajen sayen waɗannan kayan tsaftar jinin al’adar daga kamfanin cikin gida mai suna Uniglory Nigeria Limited da ke Ikorodu, Legas.

“Wannan yana nuna yadda gwamnati ke ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma kula da buƙatun ‘yan ƙasa”.

Tayi kira ga hukumomi, kamfanoni, da ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su shiga cikin wannan shiri domin taimakawa ‘yan mata masu buƙata.

Hakazalika ta roƙi sarakunan gargajiya, malamai, da shugabannin al’umma da su ba da goyon baya ga wannan shiri, musamman wajen tabbatar da sun sa ido wajen rabon kayan, tare da tabbatar da cewa ‘yan matan da suka cancanci a basu ne kawai suka amfana.

Ta Kuma bayyana cewar kayan tsaftar jinin al’adar kyauta ce. Tana mai gargaɗin cewar kada a samu wani rahoton yunƙurin sayar dasu.

“Munyi hakan ne don tabbatar da kun cigaba da zuwa makaranta, ku dage da karatu, ku taimaki juna, kuma kada kunya ta hana ku samun ƙwarin gwiwa, Ku yi amfani da wannan dama domin cika burinku, domin ku ne gobe ta Najeriya”.

“A ƙarshe, ina kira ga kowa da kowa da mu ɗauki alhakin kare mutunci, lafiya, da makomar ‘yan mata a ƙasarmu tare da mun tabbatar kowace yarinya tana da damar rayuwa cikin kwanciyar hankali, samun ilimi da ci gaba”. Madam Remi Tinubu ta ƙara da cewa.

By ukarofi