Yadda aka tada jijiyar wuya tsakanin Wike da sojoji kan fili a Abuja

Spread the love

Wani jami’in soja a Abuja ya yi gaba da gaba da Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, inda ya hana shi shiga wani fili da aka ajiye sojoji domin tsaron sa.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da Wike ya nace akan cewa sai ya shiga filin inda ya fuskanci jami’in sojan da ya ce umurni aka ba shi da kada ya bari kowa ya shiga wannan wurin.

Jami’in ya ƙara da cewa yana aiki ne da umarni, don haka babu yadda zai yi ya ba shi damar shiga filin.

An jiyo Minista Wike yana bai wa jami’in umarni da ya yi shiru, amma da zarar sojan ya buɗe baki sai ya ce shi ba ƙaramin soja ba ne, don haka ba zai yi shiru ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, filin, wanda aka katange da Wike ya nemi shiga, wanda aka katange, ana kyautata zaton na wani babban soja ne ke da shi.

Bayan haka ne sai ministan ya zargi jami’an nuna jiji da kai, lamarin da ke nuna sun fi ƙarfin doka ta yi aiki akansu, kamar yadda ya nuna.

Wike ya kuma ce babu wata takarda da ke nuna cewa filin mallakinsu ne don haka ya sa suka je wajen domin gano da ido, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci haka ba.

By Babaji