Fatima Yusuf Muhammad ta kasance mace mara kasala wajen fafutikar neman ilimi, sana’ar dogaro da kai da kuma faɗakar da al’umma da nishaɗantar da su ta hanyar rubuce-rubucen littattafan hikaya. A wannan makon Manhaja ta yi wa masu karatu kiciɓis da ita don jin yadda ta ke jifar tsuntsaye uku da dutse ɗaya, ma’ana ga neman ilimi da ta sa gaba, sana’a da kuma rubutu, ga kuma ɗawainiyar iyali. Kai, wani aiki dai sai mai shi. Ga yadda tattaunar ta kasance:
Masu karatu zasu so jin tarihin ki.
Ni dai suna na Fatima Yusuf Muhammad. An haife ni a garin Kaugama da ke Jihar Jigawa. Ni Bahaɗejiya ce. Na yi karatun firamare da sakandare, kuma na yi ƙarama da babbar difiloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, wato Kaduna Polytechnic. Na yi karatun addini ibtida’iyya, mutawassiɗa da thanawiyya. Na yi karatun ‘basic’, ‘intermediate’ da ‘advanced certificate’ a harshen Larabci, na kuma yi difiloma duka a harshen na Larabci. Yanzu haka kuma ni ɗaliba ce a Buɗaɗɗiyar Jami’a ta Nijeriya, wato ‘National Open University of Nigeria’ da ke Kaduna, ina karantar B.A. Islamic Studies.
Ko malama ta na da iyali?
Ina da su. Ina da miji da yara shida – huɗu mata, biyu maza. Har da jikoki guda biyu. Ina zaune ne a ƙwaryar Kaduna.
Mecece sana’ar ki?
Ni dai zan kira kai na jaura goma maganin mai gasa. Ni dai marubuciya ce, malamar makaranta, kuma ina saye da sayarwa, don ba maraya sai rago. Duk wadda ta zauna, za ta ga zaunau.
Ko za mu iya sanin wace malama ce ke?
Qwarai kuwa, ni malama ce ta Islamiyya. Ina karantar da matan aure da tsofaffi da kuma yara.
Wane irin saye da sayarwa ki ke yi?
Ina sana’ar sayar da turaruka na ruwa da na wuta da na tsinke, humra da duk wani nau’i na turaren qamshi. Ina sayar da albasa, kayan shafe-shafe da kuma duk wani abu da ya tari gaba na idan dai na san zan samu qaruwa mai albarka a cikin sa.
Wasu na ganin kamar zurfin ilimi ga ‘ya mace ba shi da amfani. Me za ki ce kan wannan?
Wannan ba gaskiya ba ne. Ai ita mace jami’a ce, ko na ce makwankwaɗar ilimi ce, idan ba ta da zurfin ilimi ai za a samu tazgaro. Ilimin mace ai shi ne mafi alfanu saboda ƙarancin ilmin ta na iya jawo mishkila a cikin ahalin ta da kuma zamantakewar ta da jama’a.
A zamantakewar aure, wa ya fi wahala tsakanin miji da mata?
Zahiri namiji shi ne mafi shan wahala domin shi ke fita nema domin kare mutuncin iyalin sa.
Menene matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani?
Matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani shi ne domin kare mutuncin ta na rayuwa da kuma tallafa wa iyalin ta da kauce wa dukkan wani abu da zai taso mata wanda ba sai ta jira an yi mata ba. Ga kuma yadda rayuwa ta ta’azzara, saboda haka nema ya zama tilas. Babu maraya sai rago.
Menene burin ki a fagen rubutu nan gaba?
In ga na zamanto wata tauraruwa, rubutu na ya amfani duniya da al’umma ta baki ɗaya, ya kasance ko bayan ba ni idan an ɗauko rubutu na za a tuna ni da shi, tunani na alheri.
Kin taɓa samun karramawa a fagen rubutu?
Na taɓa samun karramawa sau ɗaya.
A matsayin ki na mace, kin sami ƙalubale a tafiyar sana’ar ki?
Sosai ma kuwa, musamman ta ɓangaren rubutu tsakanin mu da ‘yan kasuwa: ka sa kuɗi ka buga littafi, kuɗin ka su maƙale; kura da shan bugu gardi da amshe kuɗi!
Nasarori fa?
Na samu nasarori masu yawa. Na san mutane da dama, mutane sun san ni. Abubuwan ba su misaltuwa.
Wasu na ganin kishiya abin tsoro ce. Yaya zancen ya ke a naki ɓangaren?
Sam, kishiya ba abar tsoro ba ce, abokiyar zama ce, kuma ƙaimi ce. Kishi ai mutum ya nemi na kan sa, kowa kuma da halin sa zai zauna. Idan ba a ƙari mu wa zai auri namu? Kuma kai ka isa ka haramta abin da Allah ya halatta? Ni a wuri na kishiya ba wata aba ba ce.
Wane abinci ki ka fi son ci?
Ina son abincin gargajiya, musamman ma tuwo da miyar kuka.
Wace shawara za ki ba matan da ba su sana’a?
Shawara ta ita ce su tashi su nemi na kan su. Na ƙara faɗa: ba maraya sai rago, kowa ya zauna zai ga zaunau. Sana’a rufin asiri ce. Hajiya Barmani Coge ta ce, “Duk wadda ba ta sana’a aura ce, sakara bankaurar banza, ta saida gulma ta sai tabarma, ta shimfiɗa ta ji daɗin tsegumi”.
Ya aka yi ki ka iya tauna taura biyu ko ma in ce uku a lokaci xaya, wato sana’a, karatu da rubutu?
Da taimakon Ubangiji, da kuma sa kai, da jajircewa, da son abin a zuciya, samun dama, an ce “idan ka samu dama ka dama kafin masu damu su dame ka”. Uwa-uba kuma da samun goyon baya da tallafi daga gurin abokin zama.
Wace kala ki ka fi so?
Ina son kalar kore da kuma shuɗi.
Me ke saurin ɓata maki rai?
Idan aka sava wa Allah ko kuma aka soki Manzon Allah (S.A.W.).
Ko akwai wani abu da ya taɓa ba ki mamaki da ba za ki tava mantawa da shi ba?
Akwai su da dama.
Za mu iya sanin ɗaya daga cikin su?
Yawan sanin jama’a, saboda na yi hulɗa da mutane da dama, kuma kowanne za ki ga da irin halin sa.
Wane irin kaya ki ka fi sha’awar sawa?
Ina son doguwar riga.
Ko malama na taɓa siyasa?
Ban taɓa yi ba gaskiya.
Mata da yawa na sha’awar fara sana’ar sayar da turare kasancewar ta mai riba biyu (ka sayar ka kuma shafa) amma su na ƙorafin ba su da jarin da zai isa yin sana’ar, a cewar su ba a yin ta da kuɗi ƙalilan. Shin ya zancen ya ke?
Haka yake, amma wannan hasashen nasu ba gaskiya ba ne. Da jari ƙalilan ma za ka iya jan jari. Ai da yayyafi kogi kan cika. Kuma sana’ar turare ta na da riba.
Macen da ba ta da jari kuma ta na son yin sana’a, ya za ta yi?
To, ina ganin sai ta nemi tallafi daga makusantan ta ko kuma ta nema daga wurin gwamnati ko kuma ‘yan ƙungiyoyin da ke tallafa wa masu ƙananan sana’o’i.
To, mun gode ƙwarai da gaske.
Ni ke da godiya.
