Daga WAKILINMU
Gobara ta kama katafaren shagon zamanin nan da ke Abuja da aka fi sani da ‘Ebeano Supermarket’ da ke yankin Lokogoma-Apo a birnin tarayya.
Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a kan dalilin tashin gobarar.
An ga jami’an kwana-kwana a yankin inda suka yi ƙoƙarin kashe gobarar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Abuja, Ibrahim Muhammad, ya tabbatar da faruwar ibtila’in wanda ya auku jiya Asabar da daddare.
