Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya dakatar da shirin cire tallafin fetur

Spread the love

Gwmanatin Tarayya ta bayyana dakatar da shirinta na janye tallafin fetur har sai abin da Allah Ya yi.

Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yau a Abuja.

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan sabbin kafofin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, dakatar da shirin ya biyo bayan rashin goyon baya da Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna ne kan cire tallafin na fetur.

By Editor