2023: Ku haɗa kanku don samar da nagartaccen shugabanci, kiran Buhari ga gwamnonin APC

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamnonin APC da su zamo madu kiyaye ƙa’idojin jam’iyya yayin zaɓen fidda gwani na APC mai zuwa.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin wata ganawa da ya yi da gwamnonin na APC su 22 haɗe da Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ranar Talata a fadar Villa da ke Abuja.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya ce Shugaba Buharin ya ce, “Shirye-shiryen zaɓen 2023 sun kankama, kuma a sanina galibin nasarar jam’iyyun siyasa a sassan duniya ya danganta ne da irin nagartaccen shugabancin da suke da shi.

“Jam’iyyarmu ta APC ma a kan haka take, inda muke ci gaba da aiwatar da tsare-tsarenmu don samar da nagartacciyar ƙasa.”

Buhari ya ƙara da cewa, “Yayin da na soma shekarar ƙarshe a wa’adin mulkina na biyu a matsayin Shugaban Tarayyar Nijeriya kuma shugaba a jam’iyya, na ga akwai buƙatar in tabbatar da an samu shugabanci mai ƙarfi ga jam’iyya tare da tabbatar da hakan ya auku bisa tsari.

“Akwai buƙatar irin wannan shugabancin ne don ƙarƙo da kuma haɗin kan jam’iyya.

“Haka nan, akwai buƙatar hakan don bunƙasa sha’anin zaɓenmu ta hanyar tabbatar da jam’iyyarmu ce ke riƙe da mulki da kuma samun mafi yawan ‘yan majalisu haɗe da ƙarin jihohi.”

A cewar Buhari, “Nan da ‘yan kwanaki jam’iyyarmu za ta gudanar da babban taronta wanda a nan ne kuma za ta yi zaɓen fidda gwani don tsayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa yayin Babban Zaɓen 2023.

”Wannan muhimmin al’amari ne wanda ya kamata sakamakonsa ya nuna wa duniya ingancin APC a fagen dimokuraɗiyya.”

By Editor