Daga CMG HAUSA
Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar kafa kungiyar ƙasa da ƙasa ta tattauna batutuwan da suka shafi kafar intanet.
Xi Jinping ya jaddada cewa, kafar intanet na da alaka da makomar bil adama. Kuma Sin ta shirya haɗa hannu da kasa da ƙasa wajen ɗaukar ƙungiyar a matsayin wata muhimmiyar dama ta inganta tabbatar da kafar ta intanet ta kasance buɗɗaɗiya mai cike da tsaro da tabbatar da adalci, kuma mai ƙwari da kuzari, ta yadda jama’a a faɗin duniya za su amfana.
An gudanar da taron ƙaddamar da ƙungiyar ne yau, a birnin Beijing.
Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
