SON ta haɗa kai da Kwastam don yaƙar shigo da kaya marasa inganci

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tabbatar da ingancin kaya ta Nijeriya (SON), sun haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da hukumar hana fasa-ƙwauri (Kwastam) domin yaƙar shigo da kayayyaki marasa inganci cikin ƙasar nan.

Darakta janar na hukumar SON, Mallam Farouk Salim, a yayin wata ziyara da kai zuwa Shalkwatar Kwastam a Abuja, ya jaddada irin muhimmiyar rawar da hukumar ta Kwastam take takawa a wajen yaƙi da shigo da kayayyaki marasa inganci a Nijeriya.

Hakazalika, Mista Salim ya nuna yabawarsa ga irin gudunmawar da jami’an hukumar suka ba hukumarsu a baya, kuma suna sa ran su yi musu abinda ya fi haka a gaba musamman yanzu da suka dawo tashoshin teku.

Shi ma a nasa jawabin, Kwanturolan rundunar jami’an Kwastam ɗin Alhaji Hameed Ali, ya bayyana cewa, tabbas haɗakar waɗannan ɓangarorin za ta taka rawar gani wajen kare ƙasar na da ma al’ummarta.

Ali ya ƙara da cewa, akwai buƙatar jami’an hukumar SON su ma su faɗaɗa iliminsu na sanin fasahar zamani, su kuma jami’an hukumar Kwastam su samomu horaswa a ɓangaren sanin aikin tantance ingancin kaya domin samun daidaito.

Shi dai wannan taro an shirya shi ne domin jawo hukumar Kwastam ta Nijeriya don samun haɗin kanta wajen kare tattalin arzikin ƙasa ta hanyar inganta cinikayya, samar da haraji, da kuma hana fasa-ƙwauri, da kuma yaƙi da shigo da kaya marasa inganci ƙasar nan ta hanyar haɗa gwiwa da hukumar SON.

By Editor