Daga AISHA ASAS
Gwamnatin Mali ta bai wa kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Ƙasar Olivier Salgado kwanaki uku ya fitce daga ƙasar saboda wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na twitter.
Sanarwar gwamnati ta ce, kakakin MINUSMA, na da sa’o’i 72 ya bar ƙasar kan wasu mukamai da ta ce ba abin lamunta ba ne dangane da taƙaddama da ta shafi sojojin Ivory Coast.
Korar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saƙa tsakanin sojojin da ke mulkin Mali da kuma abokan hulɗar ƙasa da ƙasa da ke goyon bayan yawin da ƙasar ke yi da masu iƙirarin jihadi.
Saqon Salgado, ɗan Ƙasar Faransa, na da alaƙa da sojojin Ivory Coast 49 da aka tsare bayan saukar su a filin jirgin saman Bamako a ranar 10 ga watan Yuli.
Hukumomin ƙasar dai na zargin sojojin da zama ‘yan amshin shata. Sai dai Ivory Coast ta ce an aike su ne domin ba da gudunmawar goyon baya ga MINUSMA, a ƙarƙashin tsarin karɓa-karɓa.
