Tarihin da Ahmed Musa ya kafa masu wahalar karyawa a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ahmed Musa, ya fara buga wa Super Eagles ta Nijeriya wasa ne a ranar 5 ga watan Agustan 2010, inda ya shiga wasan ne a canjin Mikel John Obi, a wasan da suka doke Madagascar da ci 2-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON na shekarar 2012.

Ya buga gasar AFCON guda uku (2013, 2019 da 2021).

Ya samu nasarar lashe guda daya a cikin 2013 AFCON.

Sannan ya buga gasar cin kofin duniya guda biyu (2014 da 2018).

Musa shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a ragar Nijeriya a gasar cin kofin duniya da ya ci ƙwallaye 4. Ya zama ɗan Nijeriya na farko da ya ci fiye da sau ɗaya a gasar cin kofin duniya ta FIFA, bayan ya zura ƙwallaye biyu a ragar Argentina a gasar cin kofin duniya ta 2014.

Ya kuma zama ɗan Nijeriya na farko da ya zura ƙwallo a gasar cin kofin duniya ta FIFA guda biyu, bayan ya zura ƙwallaye biyu a ragar Iceland a matakin rukuni na gasar cin kofin duniya ta 2018.

A watan Nuwamba 2021, ya zarce tarihin Joseph Yobo da Vincent Enyeama na mafi yawan buga wasanni da 101 ya zama ɗan wasan da ya fi kowa taka leda a Nijeriya. A halin yanzu yana da wasanni 107 na ƙasa da ƙasa.

By Editor