Kowace ƙwarya tana da abokin burminta

Spread the love

Daga BELLO WANG

A kwanakin baya, na zanta da wasu masana a yayin wani taro da ya gudana a birnin Beijing, ƙarƙashin laimar dandalin masanan Sin da Afirka, inda kalaman da wani masani dan ƙasar Habasha mai suna Yonas Adaye ya yi, ya burge ni matuƙa.

Ya ce, “sakamakon bambancin al’adu da tarihi, ba za samu wani tsarin raya ƙasa da zai biya buƙatun dukkan ƙasashe ba. Wasu ƙasashen yamma na ganin cewa, ‘Ba za a samu nasarar tafiyar da harkokin mulki ba, idan ba a rungumi tsarinmu ba.’

Amma ƙasashen Afirka ba za su ci gaba da amincewa da ra’ayinsu ba.” Na yarda da ra’ayin masanin. Saboda idan muka nazarci fasahohin da kasar Sin ta samu, to, dole ne duk wata ƙasa mai tasowa ta yi kokarin bin turbar raya ƙasa ta kanta, kafin ta iya samun ci gaba mai ɗorewa.

Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin a shekarar 1949, kasar ta nace da zama ƙarƙashin mulkin jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, da turbar tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta Sin.

Hakan a ganin ƙasashen yamma, wai “mulkin kama ƙarya” ne. Sai dai sakamakon da ƙasar Sin ta samu karkashin turbar da ta tsara da kanta, shi ne ya haifar da ci gaban tattalin arzikinta.

Wani masani a ƙasar Afirka ya taba bayyana cewa, “ Jimillar GDPn ƙasar Kenya ta fi ta ƙasar Sin yawa, a shekarar 1961. Amma zuwa shekarar 2020, GDPn Kenya ya ƙaru da ninki 3, yayin da jimillar ta ƙasar Sin ta karu da ninki 50.” Kalamansa sun shaida cewa, turbar da ƙasar Sin ta zaba, ita ce daidai.

Cikin shekaru 5 da suka wuce, duniyarmu ta yi fama da koma bayan tattalin arziki. Inda aka fuskanci tarin ƙalubaloli, da tsanantar rikici tsakanin wasu ƙasashe, ko tsakanin al’ummomin wata ƙasa. Amma ƙasar Sin tana bin hanyarta ta neman ci gaba yadda ya kamata. Wasu abubuwan da na gani da ido su ne: Mazauna ƙauyuka sun samu wadata ta hanyar raya harkar yawon shaƙatawa, ko kuma tallata amfanin gona ta kafar Internet.

Yayin da a cikin birane, ana samun ƙarin itatuwa da bishiyoyi, da kyautatuwar muhallin zama. Kana ‘yan saman jannatin ƙasar Sin suna zirga-zirga a sararin samaniya ta cikin kumbunan ƙasar. Ban da wannan kuma, ƙasar ta yi nasarar shawo kan yaduwar cutar COVID-19, da maido da ayyuka masu alaƙa da tattalin arziki cikin sauri.

Haka zalika, a yankin Hong Kong na ƙasar, ƙasar Amurka ta ci tura a yunƙurin na ta da tarzoma, da juyin juya hali, inda aka maido da kwanciyar hankali a yankin, bisa matakan shari’a da ƙasar Sin ta ɗauka. Ban da wannan kuma, na ga yadda ƙasar Sin ta iya kare cikakkun yankunanta daga ƙasar da take nuna fin karfi a duniya.

Kana abu mai muhimmanci shi ne, na ga yadda Sinawa suke nuna cikakken imani kan turbarsu, inda ko da yake suna ƙoƙarin tinkarar matakan wasu ƙasashe na neman shafawa ƙasar Sin bakin fenti, da hana ta samun ci gaba, a hannu guda kuma suna nacewa kan akidar al’ummar dan Adam mai makomar bai ɗaya, da hadin gwiwa don moriyar dukkan ɓangarori.

Hausawa su kan ce, “Ko wace ƙwarya tana da abokin burminta”, kana “ Kayan aro ba ya rufe katara.” Idan mun ce ƙasar Sin na da wani asiri na raya kai, to wannan shi ne zabin turbar da ta dace da yanayin ƙasa, da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali, gami da raya tattalin arziki.

Idan al’ummar wata ƙasa suna iya kiyaye wani yanayi na haɗin kai da juna, a ƙoƙarin raya kasarsu, ba tare da ta da zaune-tsaye ba, to, duk wani ƙalubale, ba zai iya hana ƙasar samun ci gaba ba.

By Editor