Taron ofishin siyasa na kwamitin ƙolin JKS ya gabatar da shawarar ayyana ranar buɗe babban taron wakilan jam’iyyar karo na 20

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ya gudanar da zama a Talatar nan, a wani ɓangare na tsara ayyukan cikakken zama na 7 na kwamitin tsakiya na 19 na JKS, da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20.

Zaman ya amince da bude cikakken zama na 7, na kwamitin tsakiyar JKS na 19 a ranar 9 ga watan Oktoba a nan birnin Beijing, inda ofishin siyasa na kwamitin tsakiya zai ba da shawarar buɗe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20, a ranar 16 ga watan Oktoba dake tafe a birnin na Beijing.

Fassarawar Saminu Alhassan

By Editor