Daga CMG HAUSA
Ƙasar Sin ta yi watsi da rahoton da MƊD ta fitar, game da batun kare haƙƙoƙin bil Adama a jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, tana mai bayyana rahoton da tarin ƙarairayi, waɗanda aka kitsa domin amfani da su a matsayin makamin siyasar Amurka da ƙasashen yamma.
Da yake tsokaci game da hakan a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce fitar da rahoton mai cike da rashin gaskiya, da ofishin babban kwamishinan MƊD mai lura da kare haƙƙoƙin bil Adama ya yi, ya tozarta darajar ofishin.
Mai fassara: Saminu