Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Zauren Al’ummar Hausawan Duniya, cikin bukuwan ranar Hausawan Duniya ta kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ziyara, tare da zaɓarsa a matsayin uban wannan ƙungiya.
Cikin jawabinsa na maraba, Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya nuna godiyarsa ga Allah ya ba da ikon kaɓar baƙuncin waɗannan baƙi nasa.
Mai Martaba Sarki ya ce, “muna miƙa matuƙar godiyar mu ga Allah da ya ba mu ikon ganin wannan rana cikin ƙoshin lafiya har muka karɓi baƙuncin ku. Muna godiya ga Allah da ya kawo ku lafiya, tate da fatan za ku koma lafiya.”
Haka kuma Sarkin ya nuna farin cikinsa da zaɓarsa da aka yi a matsayin Uba na wannan ƙungiya ta Zauren al’ummar Hausawan Duniya, “ba abin da za mu ce sai dai Allah saka maku da alhairi,” in ji Sarki.
Ya ci gaba da bayyana cewa saboda muhimmancin wannan rana da kuma al’ummar Hausan Duniya, “ya zama wajibi a gare mu mu karɓi wannan girma da aka ɗora mana. Tare da fatan Allah zai mana luɗufi ya ba mu ikon ɗauka,” In ji Sarkin na Zazzau.
Cikin zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wannan ziyara, Shugaban zauren Hausa ta duniya, Ambasada Muhammad Kabir Gure ya bayyana cewa sun zaɓi kawo wannan ziyara a wannan rana ce domin muhimmancin ranar, wacce ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware don Hausan duniya.
“Wannan muhimmiyar rana ce a gare mu, shi ne muka kawo wa Mai martaba Sarkin Zazzau ziyara domin ya sanya mana albarka. Kuma a matsayinsa na Uba, ya sa mu ka zo neman albarka, wanda kuma a yanzu haka mun ba shi matsayin Uba na wannan ƙungiya,” in ji Ambasada.
Shugaban ya ci gaba da bayyana cewa, wannan ziyara ta su ta kasance ne tamkar jaje ko nuna alhini bisa abubuwan da suke faruwa ga al’ummar Hausawa marasa daɗi, wanda ya ce wajibi ne ga dukkan mai kishi ya nuna rashin jin daɗinsa game da waɗannan abubuwa.
Shi ma a nasa tsokacin, Shugaban wannan zauren Hausa na jihar Kaduna, Alhaji Sanusi Sirajo ya bayyana cewa, “mun zo ne mu nuna alhini game da al’ummar mu, wasu na ɗaure a dazuka, wasu ma ba a san inda suke ba. “
Alhaji Sanusi ya ƙara da cewa a halin da ake ciki, Bahaushe bai isa ya tashi ya yi doguwar tafiya cikin kwanciyar hankali ba, “saboda haka sai muka ga ashe ke nan ba biki ya kamata mu yi ba, alhini za mu nuna, ai ranar bikinmu, ita ce ranar da ‘yan uwanmu suka fito daga daji,” in ji shi.
Ya ce, wannan ne ya sa suka zo wurin mai martaba Sarkin Zazzau domin jajanta wa juna, tare da yin kira ga gwamnati ta hanzarta karɓo mutanenmu da ke dazuka.
