Daga CMG HAUSA
Ma’aikatar aikin gona da ƙauyuka ta ƙasar Sin ta sanar a kwanan baya cewa, an riga an kammala aikin girbin hatsi a gonaki fiye da kadada 11,333,333 a ƙasar Sin, jamillar da ta kai kashi 13.3% na ɗaukacin gonakin ƙasar da ake noman hatsi a ciki, a wannan lokacin kaka.
Ban da wannan kuma, wakilin CMG ya lura da muhimmiyar rawar da inshorar aikin gona ke takawa a fannin tabbatar da samun girbi mai armashi, inda kamfanonin inshora suke ba da tallafi ga manoma wajen tinkarar bala’i daga indallahi.
Sa’an nan a lokacin da manoma suka samu hasara sakamakon iftila’i, kamfanonin za su biya su diyya.
Mai fassara: Bello Wang
