Gamayyar magoya bayan APC ta tsige shugabanta na ƙasa

APC
Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Jam’iyyar APC ta tsige shigabanta na ƙasa, Jelil Adewale Adeogun, saboda rashin gansuwa da salon shugabancinsa.

Sun cimma matsayar tsige shugaban nasu ne a wajen taron da tsohon sakataren gamayyar, Malam Dattijo Danjuma Miya ya shirya ranar Talata a Abuja.

Rashin tafiya da kowa na daga cikin dalilan da suka sanya gammayar tsige Adeogun.

Tuni dai gamayyar ta zaɓi Dr. Ahmad Saleh a matsayin sabon shugabanta, Emmanuel Nwosu a matsayin sakatare, sannan Mubarak Mohammed a matsayin mataimakin sakatare.

Sauran sun haɗa da Atir Solomon, shugaban shiyyar Arewa, Larai Kolo, ma’aji, Samira Ibrahim, shugabar mata ta ƙasa, Dr. Kabir Muhammed, shugaban shiyyar Arewa maso-Yamma da kuma Iso Bassey a matsayin shugaban matasa na ƙasa.

Barista Noble Agbaeze, odita na ƙasa, Dattijo Danjuma, sakataren tsare-tsare, Lawal Ibrahim, mataimakin shugaban matasa, sai kuma Tope Najeem a matsayin shugaban shiyyar Arewa ta tsakiya.

Sabon sakataren gamayyar, Emmanuel Nwosu, ya buƙaci babban ofishin APC na ƙasa da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar da su daina mu’amala da tsigaggen shugaban face sabbin shugabannin da aka naɗa.

Mahalarta taron sun haɗa da Engr. Emmanuel Nwosu, Atir Solomon, Barr. Noble Agbaeze, Kwamanda Alhassan (mai murabus), Dr. Kabir Muhammad, Hajiya Larai Kolo, Hajiya Samira Ibrahim, Dr. Ahmad Saleh, Lawal Ibrahim, Najeem Tope, Yahya Momoh da kuma Mubarak Mohammed.

By Editor