Daga CMG HAUSA
Yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya shirya taron manema labaran da aka saba gudanarwa.
Kuma wani dan jarida ya gabatar da tambaya cewa, a kwanakin nan, wani binciken jin ra’ayin jama’a da wata hukumar jin ra’ayin jama’a ta ƙasar Burtaniya da ake kira YouGov ta yi, ya nuna cewa, a shekarun baya, al’ummar Afirka sun kara nuna sha’awarsu ga ƙasar Sin.
Adadin ‘yan ƙasashen Najeriya da Kenya da Afirka ta kudu da Masar da aka zanta da su, waɗanda ke ganin ƙasar Sin tana da matuƙar tasiri kan harkoki na ƙasa da ƙasa, ya kai kaso 83 cikin 100 da kaso 82 da 61 da kuma kaso 57 cikin 100 bi da bi, ƙaruwar kaso 15 da kaso 24 da kaso 13 da kaso 10 cikin 100 bi da bi kan na shekarar da ta gabata.
Shin mene ne ra’ayinka kan wannan batu?
Zhao Lijian ya ba da amsa cewa, sakamakon ƙuri’ar jin ra’ayin jama’ar da ka ambata, ya sake tabbatar da cewa, alaƙar Sin da Afirka, ta kawo wa jama’ar Afirka alheri a zahiri, kuma jama’ar Afirka sun yi maraba da ma na’am da su.
Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
