Zaɓen 2023: An kai wa ma’aikatan EFCC hari a Abuja da Imo

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Wasu tsageru sun kai wa wasu ma’aikatan hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, waɗanda ke aikin saka ido a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu, hari a kusa da fadar hakimin Bwari da ke birnin tarayya.

Lamarin ya biyo bayan kame da aka yi na wanda ake zargi da ƙwarewa wurin siyen ƙuri’un zaɓe a mazaɓar da ke Science Primary School, Bwari.

Ma’aikatan na EFCC sun yi nasarar damƙe wanda ake zargi, mai kimanin shekaru 30, kuma a tare da shi akwai jerin sunayen waɗanda aka riga aka siye ƙuri’unsu har ma ya tura masu kuɗaden ta hanyar taransifa.

A daidai lokacin da ma’aikatan suka yi yunƙurin ficewa da mutumin ne ‘yan daban suka farmasu, tare farfasa motocinsu na aiki.

Amon harbin bindiga da ma’aikatan suka yi ne ya sa tsagerun ja-baya, wanda hakan ne ya ba su kariya har zuwo lokacin da jami’an tsaro na ‘yan sanda da kuma na farar hula suka iso wurin.

Haka zalika irin wannan lamarin ya faru a Jihar Imo, a wata rumfa mai lamba 001 da ke wata makarantar firamare da ke bayan layin Chorobim.

An ruwaito cewa, wasu mutane da suke cikin mota ƙirar SUV da kuma farar Hilux sun yi wa ma’aikatan Hukumar EFCC ɓarin wuta. Mutanen da ake zargi da siyan ƙuri’un jama’a a rumfar sun yi nasarar harbe wasu daga cikin ma’aikatan na EFCC ne a daidai lokacin da ma’aikatan suka gano takon nasu.

Lamarin dai ya wakana ne a wajen ita wannan mazaɓar inda cikin azama jami’an suka fara mayar da martani, wanda hakan ya tilastawa mutanen tserewa tun kan isowar jami’an tsaro.

By Editor