Ubangiji ya gaya min kotun sama za ta tabbatar wa Abba mulkin Kano, inji limamin coci

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban cocin Wisdom Church of Christ International, Prophet Bisi Olujobi, ya bayyana cewa, Ubangijinsa ya sanar da shi cewa, Gwamnan Jihar Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida), ya samu tagomashi a kotun sama, inda za ta rushe hukuncin baya na Kotun Zaɓen Gwamnan Jihar Kano na 2023, wacce ta sauke shi daga mulki kuma ta ɗora ɗan takarar gwamna na babbar jam’iyyar adawa a jihar, Nasiru Yusuf Gawuna.

Prophet Olujobi ya bayyana hakan ne a a jiya Alhamis a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, yana mai cewa, hukuncin sauke Abba Gida-gida da kotun zaɓe ta yi ba zai ɗore ba.

A ta bakinsa, “akwai abin jan hankali da zai faru a Jihar Kano, domin Gwamna Abba Kabir Yusuf zai cigaba da zama akan mulki bayan ɗaukakar hukuncin kotun zaɓe. Shi ne zai yi farin ciki a ƙarshen al’amari.”

Idan za a iya tunawa, a makon jiya ne Kotun Zaɓen Gwamna ta soke halascin zaven Gwamna Abba tana mai cewa, shi da jam’iyyarsa ta NNPP sun tafka gagarumin maguɗi na ƙuri’u sama da 165,000. Don haka ta ayyana Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaven da halastattun quri’un da suka bayar da ratar fiye 30,000.

Hakan ya ƙara janyo cece-kuce da hayaniya tare da ɗumamar siyasar Jihar Kano, inda yayin da wasu ke danganta hakan da fin ƙarfi daga ‘sama’, wasu kuwa ke kallon lamarin a matsayin sakaci a wajen tunkarar shari’a daga vangaren Abba da jam’iyyarsa.

A yayin da kotun ke yanke hukuncin ta hanyar manhajar Zoom, ɗaya daga cikin alƙalan kotun ya ayyana mabiya NNPP da Kwankwasiyya masu saka jar hula a matsayin ’yan bindiga ko ’yan ta’adda, saboda barazanar da wasu daga cikin jagororinsu suka yi wa rayukan alƙalan matuƙar ba su yanke hukuncin da ya yi musu daɗi ba, wanda suke kallo a matsayin shine na gaskiya.

Yayin da limamin cocin, Bisi Olujobi, ya ke taɓo batun siyasar jihohin Ondo da Edo kuwa, ya ja kunnen Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ne, sannan ya yi wa Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shuaibu, albishir.

Ya ce, abu ne mai matuƙar wahala ga Aiyedatiwa ya gaji Gwamna Rotimi Akeredolu a 2024, yana mai ƙara da yi wa Akeredolu addu’ar fatan ganin ya kammala mulkinsa, sannan ya tuno da yadda tun asali ya shawarci mataimakin nasa da ya bi a sannu, kuma ya zama mai ankara da yanayi tare da yin addu’o’i, domin ya hango afkuwar “wata rigima ta rana-tsaka”.

“na gan shi ana tsige shi bakatatan daga yanzu zuwa kowane lokaci kuma hakan zai kawo ƙarshen siyasarsa a Jihar Ondo ɗungurugum,” inji shi.

Yayin da ya juya ga batun siyasar Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Shiaibu kuwa, faston ya ce, “Ubangiji Jehovah zai kawo wasu mutane masu muhimmanci da za su dage akansa ba tare da la’akari da daga inda rikicin ya taso ba.”

Don haka sai ya buqaci Shuaibu da ya dage kan yin addu’a yana mai cewa, “ya kamata Shuaibu ya gode wa Allah kuma ya sa ido kan jami’an tsaronsa, domin na ga cewa, rikicin ba zai yi nisa ba. Yana da kyakkyawar makoma ta gadon kujerar gwamnan mai ci, Godwin Obaseki.”

Idan dai za a iya tunawa, limaman coci sun saba yin irin waɗannan hasashe akan harkokin siyasa musamman a gabanin manayn zavuka a qasa da duniya bakiɗaya, inda wasu daga cikin hasashen sukan zamo gaskiya, yayin da wasu kuwa suke bin ruwa.

A Jihar Edo dai a makon jiya Mataimakiin Gwamnan ya nemi afuwar Gwamna Obaseki, inda shi kuma a jiya Alhamis ya bayar da sanarwar yafe masa, kuma tare da cigada aiki tare bayan dogon rikicin siyasa kan muradin mataimakin na tsaya wa takarar gwamna a zaɓen jihar da za a gudanar a 2024.

Sai dai kuma har yanzu ana cigaba da yin kiki-kaka a Jihar Ondo, inda Mataimakin Gwamna Aiyedatiwa ke ƙara karawa da Gwamna Akeredolu.

Shi kuwa Gwamna Abba Kabir tuni ya ayyana garzayawa ga Kotun Ɗaukaka Ƙara, don ƙalubalantar hukuncin kotun zaɓen da ta sauke shi. Lokaci ne zai tabbatar da komai.

By Editor