Ruɗani ya mamaye hukuncin kotun zaɓen Gwamnan Kaduna

*Shugaban Kotun ya kori ƙarar
*Alqalai biyu sun nemi yin tutsu?
*Gwamna Sani ya yaba wa Ashiru Kudan
*PDP ta kasa gamsuwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Daga dukkan alamu hukuncin da kotun sauraron ƙarar zaɓen kujerar Gwamnan Jihar Kaduna ta yanke ya jefa mutane da dama cikin ruɗani, inda da fari aka bayar da rahotannin da ke nuni da cewa, kotun ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba (wato inconclusive), to amma jim kaɗan bayan hakan sai kuma sababbin rahotanni suka nuna cewa, hukuncin yana magana ne akan tabbatar da Gwamna Uba Sani na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Saidai kuma ƙarin bayanin da suka cigaba da biyo baya sun nuna cewa, alƙalai biyu daga cikin ukun da suka yanke hukuncin ne suka nemi da a sake zaɓe a wasu akwatinan zave, yayin da shi kuma Shugaban Kotun Zaɓen ya yanke hukuncin korar ƙarar bakiɗayanta.

A tattaunawa da Blueprint Manhaja ta yi da lauyan APC, Barista Sunusi Musa (SAN), ya yi ƙarin haske da cewa, haƙiƙanin hukuncin kotun yana nufin an yi watsi da ƙara da PDP da ɗan takararta, Isah Ashiru Kudan, ya shigar ne.

Hukuncin wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i biyar da rabi ana karanta shi, an ga alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Victor Oviawie da Mai Shari’a K. Damlat da kuma Mai Shari’a N. Nonye, inda a babban hukuncin aka yi watsi da ƙarar, saboda ba a shigar da ita akan lokaci na kwanaki bakwai da kundin tsarin mulki ya tanada ba, duk da cewa, masu ƙara sun iyaka ƙoƙarinsu wajen tabbatar da zargin yi musu maguɗi a zaɓen.

Da yake yanke hukuncin raba gardama, Mai Shari’a Oviawie ya ce, an gabatar da sanarwar ƙarar ne tunda farko a wajen kwanaki bakwai da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada tun daga ranar da aka shigar da babbar ƙarar, inda ya ƙara da cewa, don haka an yi watsi da karar ne ɗungurugum.

Sai dai kuma Mai Shari’a K. Damlat ya bambanta da shi, inda ya bayyana a cikin nasa hukuncin da cewa, an gabatar da sanarwar farko yadda ya kamata kuma ba a yi watsi da ita ba. Saboda haka wani vangare na hukuncin raba gardama ya bayyana cewa, zaɓen gwamnan bai kammala ba, saboda akwai akwatinan zaɓe guda 22, waɗanda zaɓensu bai kammala ba kuma yawan ƙuri’un dake cikinsu ya zarce adadin ƙuri’un da Uba Sani ya zarta Ahsiru Kudan da su, wato ƙuri’a guda 10,806.

To, amma Babban Lauya Sunusi Musa ya ce, wannan ɓangaren hukuncin bai shafi ainihin hukuncin da aka yanke na korar ƙarar ba, domin hakan na nuni da cewa, PDP ta samu tangarɗa tun daga tushen shigar da ƙarar tasu ne.

To, sai dai yayin da yake mayar da martani kan hukuncin, lauyan PDP, Barista Baba Aliyu, ya ce, ba su da cikakkiyar gamsuwa kan hukuncin, domin sun nemi kotu ta ayyana ɗan takararsy ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Don haka ya ce, akwai yiwuwar za su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, don canja wannan hukunci na Kotun Zaɓe.

Gwamna Uba Sani ya bayyana farin cikinsa tare da yaba wa Ashiru:

A vangare guda, Gwamna Uba Sani, a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannunsa, ya bayyana cewa, “na yi matuƙar farin ciki da ƙasƙantar da kai da hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta yanke na tabbatar da nasarata a zaɓen Gwamnan Jihar Kaduna a 2023. Hukuncin da aka yanke na tabbatar da farin jinina a wajen al’ummar jihar Kaduna. Ina yaba wa Kotun bisa tsayuwar dakan da suka yi. Sun wadatar da haƙƙoƙinmu da aiwatar da dimokuraɗiyyar zaɓe.

“Ina kuma yabawa ɗan uwana, Hon. Isah Ashiru Kudan saboda tunkarar lotun domin ya kai kokensa. Wannan ya nuna a sarari na imaninsa ga ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma wajabcin wayewa a cikin tafiyar siyasa.”

“Ina kira ga Hon. Isah Ashiru da ‘yan jam’iyyar adawa ta jihar Kaduna da su haɗa hannu da mu domin ƙoƙarin ciyar da jihar mu gaba. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a cigaba jihar. Ba game da ɗaukakar mutum ba ne.

Jama’ar mu na son kowa ya tashi tsaye don magance ɗimbin ƙalubalen da ke addabar jihar. Idan har aka haɗa kan ‘yan siyasa, za a riƙa isar wa al’ummarmu wata alama da ke nuna cewa ina neman zaman lafiya, tsaro da cigaban jiharmu, waɗanda su ne ginshiƙin shiga harkokin siyasa.”

“Ina kira ga jam’iyyar mu masu aminci da su daidaita bikin wannan nasara. Dole ne su ɗaiɗaiku da kuma gabaɗaya su haɗa kai ’yan’uwanmu maza da mata a wasu jam’iyyun siyasa. A maimakon yin biki, sai mu yi addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki Ya ci gaba da yi mana jagora da kariyarsa. Sannan mu mai da hankali kan ayyukan da ke gaba.”

A wata sanarwar ta daban , wacceMuhammad Lawal Shehu, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kaduna, ya sanya wa hannu a ranar 28 ga Satumba, 2023, ta ce, Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yi maraba da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaɓe ta jihar Kaduna ta yanke na tabbatar da zaɓensa a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023, inda ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraciyya, bin doka da oda, tabbatar da ra’ayin jama’a da kuma tabbatar da aniyar jama’a, sama da komai, ya ce hukuncin daga Allah ne.

“A wannan rana mai cike da tarihi, na bi sahun al’ummar jihar Kaduna domin murnar wannan gagarumin nasara da aka samu ga dimokuraɗiyya,” inji Gwamnan.

Yadda zaman shari’ar ya kasance:

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan ne ya shigar da ƙara inda yake ƙalubalantar zaɓen da aka yi wa Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC.
Yayin da ko wane ɓangare ke nuna ƙwarin-gwiwa na samun nasara a hukuncin da kotun za ta sanar ranar a Alhamis, 28 ga watan Satumba 2023, bisa ga dukkan alamu ana zaman qila-wa-qala ne na walau hukuncin ya tabbatar da nasarar ta APC ko kuma akasin hakan.

An tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na jihar, don kauce wa afkuwar tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.

Tun da aka fara sauraron ƙarar a farkon watan Yuni na wannan shekara ta 2023 kan zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023, ɗimbin magoya baya sukan yi dafifi zuwa zaman kotun, domin gani da sauraron yadda ƙarar shari’ar take gudana.

A lokacin zaman kotun an riƙa tayar da jijiyar wuya tsakanin lauyoyin ɓangarorin biyu, inda kowa ke ƙoƙarin tabbatar da hujjojinsa.