Yau Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi

Yau Lahadi ake sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi bayan dawowa daga taron da ya halarta a Amurka.

Taron shi ne karo na 78 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya wanda ya gudana a birnin New York. Bayan kammala taron ne Shugaba Tinubu ya ziyarci Paris da Faransa don taƙaitaccen hutu, in ji wata majiya.

Tinubu ya iso gida ne sa’o’i kafin Ranar Samun ‘Yancin Kan Nijeriya karo na 63, sannan kawana huɗu gabanin tsunduma yajin aikin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya da takwarorinta suka shirya.

Da misalin ƙarfe 7:00am na wannan safiya ake sa ran Shugaban ya yi wa ‘yan ƙasa jawabi kai tsaye a talabijin.

A tsakanin kwana 33 da Tinubun ya yi a waje, ya ziyarci ƙasashe da suka haɗa da Jamhuriyar Benin da Faransa da Guinea-Bissau da Kenya da UK da India da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma USA.