Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Ali Pate, ya buƙaci asibitocin ƙasar da su fifita ceton rayuka fiye da kowane abu.
An dai yi ta cece-ku-ce a tsawon shekaru ga asibitocin da ke neman ‘yan sanda su kai rahoton harbin bindiga da waɗanda hatsari ya rutsa da su kafin a fara jinya, lamarin da ya kai ga rasa rayukansu a lokuta da dama.
Amma da yake magana a gidan Talabijin na Channels a wani shiri ‘Sunrise Daily’ a ranar Laraba wanda Blueprint Manhaja ke sa ido a kai, Pate ya koka da wannan lamarin kuma ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni ga asibitoci a koyaushe su ceci rayuka da farko kafin gabatar da wasu buƙatu.
“Kwanan nan akwai damuwa game da marasa lafiya da suka bayyana a wuraren gaggawa da kuma rahoton ‘yan sanda da ake tambaya game da harbi ko haɗura. Gaskiya abin takaici ne, amma a duk asibitocin koyarwa na tarayya, misali, ina Maiduguri a ƙarshen mako, sai an fara ceton rai.
“Rayuwa ta farko kuma mun sake jaddada hakan. Duk asibitocinmu na yi imani suna yin haka. Babu wani mutum da ya isa ya zo da gaggawa, ko ƙalubalen da ke barazana ga rayuwa kuma a sanya shi ya rasa ransa yayin da yake jiran rahoton ‘yan sanda.
“Ceto rayuka ya zama a farko kuma wannan ita ce alƙiblar da muka bayar; abin da za mu bi ke nan kuma muna fatan dukkan asibitoci ciki har da asibitoci masu zaman kansu za su kasance da wannan tunanin na ceton rayuka da farko,” in ji Pate.
Ministan lafiya ya ce ana sa ran jihohin ƙasar nan suma za su bi umarnin gwamnatin tarayya a asibitocin su daban-daban. Ya kuma nanata cewa asibitoci masu zaman kansu suma wajibi ne su bi wannan umarni, yana mai tunatar da su cewa a matsayinsu na ma’aikatan lafiya ceton rayuka shi ne ke kan gaba a ko’ina.
Ya kuma yi magana kan ƙudirin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa inshorar lafiya a qasar nan tare da ƙaddamar da Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA).
Pate ya ƙara da cewa samun damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai araha ga dukkan ‘yan Nijeriya yana da matuƙar muhimmanci a kan hanyar da za ta kai ga cimma nasarar samar da tallafin kiwon lafiya na duniya (UHC).
