Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
La’akari da buƙatar da ake da ita na samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf a Litinin da ta gabata, ya ƙaddamar da rabon littattafai da kayayyakin tallafin karatu ga makarantun firamare da sakandiren gwamnati a faɗin jihar a wani taron da aka gudanar a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnati.
Da yake jawabi, Gwamna Abba Kabir ya ce samar da kayayyakin ya yi daidai da kishin gwamnatinsa na inganta harkar karatu a makarantun gwamnati da kuma cika buri na al’ummar jihar, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano ta jajirce wajen ɗaukar matakan da suka kamata don farfaɗo da harkar karatu daga rugujewar da tsarin ilimi ya yi shekaru takwas da suka gabata.
A cewar Gwamnan, “mun yi imanin cewa ilimi shi ne arziki mara iyaka da kowace al’umma za ta wadata al’ummarta da shi, tare da sanya al’umma su kasance masu kishin ƙasa, masu amfani ga kansu da sauran al’umma baki ɗaya.
“Gwamnatin jihar Kano na bai wa ɓangaren ilimi fifiko kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da babban shirinta na farfaɗo da ilimi wanda ya mayar da hankali a kai, faɗaɗa hanyoyin samun ilimi, tabbatar da samar da ingantaccen ilimi da kawar da jahilci ta hanyar koyo na tsawon rai,” inji Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan ya yaba da gudunmawar da malamai ke bayarwa a ƙarƙashin shirin BESDA (Better Education Services Delivery for All).
“Ina yabawa da rawar da malaman mu na BESDA suke takawa wajen inganta karatunmu na firamare. A bisa wannan na ke cewa gwamnatin Kano za ta yi duk mai yiwuwa don taimaka musu ta kowace hanya da za ta yiwu.”
Sannan ya ba da umarnin a tantance dukkan malaman BESDA da ke faɗin jihar Kano nan da makonni biyu a shirye-shiryen ba su aikin yi.
Kayayyakin da aka rarraba sun haɗa da: Littattafan rubutu miliyan 1.3 na harshen Ingilishi, Lissafi, Kimiyya da Fasaha daga tushe, Littattafan motsa jiki 670,000, fararen alluna guda 215, Maka ta rubutu guda 7,100, jakunkuna 15,000, takalman na makarantu guda 15,000, 311, 6000 saitin kayan lissafi fensir da shafaina,
Sauran sun haɗa da; na’urorin haɗi 10,368 na ɗakin karatu, saiti 500,000, na’urorin haɓaka ilimi na musamman, 2,000 android tablets, 40,000 na uniforms, kwalin alli 10,000, kayan ɗakin gwaje-gwaje na kimiyya guda 50, na’urorin goge Allo 5,000 gami da kayan aikin fasahar zamani na ɗalibai.
Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a jihar nan da su tabbatar da yin amfani da abubuwan da aka tanada domin cimma burin da ake so na daukaka ilimi.
Sauran mutanen da suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da: Mataimakin Gwamnan Jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Isma’il Jibrin Falgore, Kwamishinan Ilimi, Umar Haruna Doguwa da Shugaban Hukumar SUBEB, Alhaji Yusuf Kabir Gaya, Babban Sakataren huukumar kula da manyan makarantun Sakandare ta jihar Kano, Dakta Kabiru Ado Zakirai da dai sauransu.
