An zo wajen: An samu manhaja mai tuve mutum tsirara!

Spread the love

TIJJANI MUSA MUHAMMAD

WAllaahi mun faɗa wajen shekaru goma sha uku baya (2010) cewa, matan Musulmi, ‘yan Arewa musamman Hausawa su kiyayi ɗora hotunansu a shafukan sada zumunta tun wancan lokacin a Fesbuk.

Ba don komai ba sai don gudun wasu waɗanda ba Musulmi ba za su iya sauke su a cikin wayoyinsu ko na’urorinsu su dinga kallon su suna sha’awarsu ko su yi wasu abubuwan da ba shikenan ba da hotunan.

Aka samu wasu a cikinmu da ba sai na ambaci suna ba mazansu da mata suka ƙalubalanci wannan jan hankali da kashedi da muka yi suna cewa muna nema mu tauye wa mata haƙƙi na nuna su ma suna da dama da ‘yanci.

A lokacin nan mata ‘yan boko aƙida da magoya bayansu suka yi alanfur da ayoyin Ƙur’ani da hadisan Manzon Allaah SAWS da muka kawo a matsayin hujja cewa haramun ne mata su dinga bayyana adonsu ga waɗanda ba muharramansu ba.

Dalilinsu wai abinda yake kawo mana ci baya ke nan a Musulunci, a Arewacin Najeriya, a al’ummar Hausawa, a ɗabi’armu da dai sauransu. Wai kar a wani hana mata sake da walwala kamar yadda sauran matan duniya ke da shi. Idonsu duk ya makance da sharrin Shaiɗan.

Aka yi gumurzu aka yi tataɓurza aka kai ruwa rana aka yi baran-baran muka raba hanya. Akwai guruf-guruf a Fesbuk da wasu dandalolin sada zumunta da ake tare a ciki na Musulmi ‘yan Arewa Hausawa da aka raba gari duk muka fiffice, gayyar ta watse.

Da yawa daga cikinmu masu ra’ayi iri ɗaya muka sake dunƙulewa muka kakkafa sabbin guruf-guruf da ya yi dai-dai da fahimtar addinimu, manufarmu da aƙidarmu kuma aka samu mata da maza da dama suka shigo mana ciki daga nan muka ɗora.

Wannan shimfiɗa ce na yi domin mutane a gane tushen wannan tashin hankalin dake tattare da maudu’in da na sawa wannan taken cewa yanzu haka (2023) an samar da App ko manhajar da ke iya tuɓe mace ko namiji ta yi musu zigidir haihuwar uwarsu, wato ‘undress app’.

Na san wasu ba za su fahimci illar wannan ci gaban mai haƙa rijiya kai tsaye ba, amma da mutum zai faɗaɗa ya kuma zurfafa tunaninsa abu ne mai sauƙi ya gano abin da muka hango fiye da shekaru 13 baya. Ko mene ne wannan abin dubawa cikin natsuwa kuwa?

Bari in fara da sanar muku cewa yanzu haka an kama wasu matasa a wani gari a Amurka sun yi amfani da fasahar nan ta AI wato ‘Artificial Intelligence’ ko in ce ƙirƙirarren Hankali na na’ura mai ƙwaƙwalwa sun yi wa wasu daga cikin ‘yammatan unguwanninsu tumɓur!

Waɗannan yara maza ba su fa bar hotunan tsiraicin nan da suka ƙirƙiro a wayoyinsu kawai ba sai suka wallafu su a yanar gizo kowa ya gani. Al’amarin da ya tashi hankalin iyaye a gari amma saboda abin ba na terere ba ne sai suka nemi jin ba’asi a wajen ‘ya’yansu matan.

Da aka gano cewa ‘yammatan nan ba su da wani laifi illa na ɗora hotunansu a shafukansu na sada zumunta wato soshiyal midiya a inda matasan nan suka je suka kwafo suka sa a App din nan, AI kuma ya gudanar da umarnin da aka ba shi na ya yi musu tuvur-tuvur.

Kun ga irinta ko? Abin da tuni muka ja hankalin matanmu su kiyayi faruwarsa kenan wasu suke ganin bekenmu cewa mu maza muna ɗora hotunanmu amma muna neman mu hana mata ‘yancin yin hakan alhali ba fin su muka yi ba. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne da namiji da mace ba ɗaya suke ba.

A lokacin da muka fahimci iya faruwar hakan ban da yi wa matanmu tsirara a kalle su tsaf kuma ta ko’ina sai da muka yi hasashen za a iya haɗa hoton mace da namiji a wani mummunar yanayi a kuma nemi kuɗin fansa in har mutum ba ya son a yi masa 6atanci, yarfe ko sharri a idon duniya.

Kai za ma a iya amfani da fuskar mace ko namiji a sa su a wata manhajar da za ta iya nuna su suna zina irin na bulu fim a kuma turawa miji ko mata ko iyaye ko wasu shuwagabanni da nufin ƙagen ga wacce ko wane nan an kama su a bidiyo suna fasiƙanci.

Duk da shike Hausawa na cewa “Ciki da gaskiya wuqa ba ta huda shi” amma irin zargi, waswas, bata suna, rashin yarda da amincewa, rashin natsuwa da makamantansu da mutum zai fuskanta kafin a gano gaskiyar lamarin ba ƙaramin tashin hankali ba ne. Ku tuna abin da ya faru ga Nana Aisha (RA).

Yanzu dai kowa sai ya shiga taitayinsa musammanma mu Musulmi da martaba, ƙima, daraja, mutumci, girma, kwarjini da dai sauransu ke da muhimmanci a gare mu da ahlinmu. Dole ne mu yi hattara don haka sirdan wani ko wata za su iya turo ƙazafi akan wani ko wata don su haddasa bala’i!

Abin ya fice duk tunanin mutum wAllaahi. Kamar yadda na ce ne a sama zamani ya zo mana da ci gaba kalakala. Amma fa ga dukkan alamu ta fuskoki da dama wannan ci gaban na mai haƙa rijiya ne! Kar kuma mu ji an yarda da komai sai an yi cikakken bincike an tabbatar da gaskiyar duk abin da ka iya fesowa! Ehe!

Tijjani Musa Muhammad, marubuci/manazarci ne. Ya rubuto daga Kano.

By Editor