Matasa sun gudanar da zanga-zanga kan rashin wutar lantarki A Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Ranar Litinin ɗin da ta gabata wata ƙungiya mai rajin kare mutuncin al’ummar yankin Kamba da kewaye mai suna Concerned Citizen a garin Kamba dake jihar Kebbi ta gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna ƙin jinin hukumar samar da wutar lantarki ta KAEDCO kan saɓa yarjejeniya da suka yi.

Malam Musa Kamba ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa zanga-zangar ta lumana ta biyo bayan saɓa yarjejeniya da suka yi tsakaninsu da ofishin Hukumar samar da wutar lantarki ta KAEDCO da ke kulawa da wannan yankin na cewa a kullum za su ba garin Kamba wuta ta sa’o’i shida amma sai hukumar ta rinka bayarda wuta ta sa’oi biyu kacal kuma a kan kuɗin da su ke biya kowane wata, wannan abin bai yi musu daɗi ba shi ne ya sanya suka ɗauki matakin aiwatar da wannan zanga-zangar lumana.

Ya ƙara da cewa sun haɗu ne a tsohuwar kasuwa suka zagaya gari inda daga ƙarshe suka tafi fadar Sarkin Shikon Kamba suka gabatar da jawabi tare miƙa masa takar dar neman ko dai a tsaya kan yarjejeniyar da suka yi ko kuma hukumar samar da wutar lantarkin ta katse wutar bakiɗaya.

Ya kuma bayyana cewa an gudanar da wannan zagayen lafiya ƙalau ba tare da an ci zarafin kowa ba ko tava dukiyoyin jama’a ba.

Wani matashi Malam Sama’ila Musa Kamba ya nuna rashin jin daɗinsa bisa ga yadda waɗansu marasa alƙibla da ke danganta wannan zanga-zangar lumana da siyasa inda ya ce wannan zanga-zangar ba abinda ya haɗa ta da siyasa illa dai waɗansu da ba sa son gaskiya ke son danganta shi da da siyasa.

Malam Sama’ila Musa Kamba ɗaya daga cikin shugabannin matasa da ke jagorancin wannan ƙungiyar ya nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda aka danganta wannan maganar wutar lantarki da siyasa, ya kuma ce duk wanda ya soki wannan lamarin ko ya danganta shi da siyasa za mu hannanta shi ga ‘yan sanda saboda duk zagayen da aka yi tare da jami’an tsaro aka yi kuma sun shaida yadda aka yi zanga-zangar ba a ci mutuncin kowa ba kuma taɓa dukiyar ba har aka watse.

Wakilinmu ya nemi jin tabakin kamfanin samarda wutar lantarkin ta hanyar jami’in hulda da jama’a inda ya bayyana MSA da cewa ba shi da labarin wannan zanga-zangar amma dai idan akwai wani bayani zai neme shi, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba amsa.

By Editor