Kotun Allah ya isa: Tsakanin Allah ya isa da Allah ya yi albarka

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Fassara ce ta Hausawa ko a ce kirari da a ke yi wa Kotun Qoli cewa “KOTUN ALLAH YA ISA” bisa ma’ana duk hukuncin da ta yanke sai dai a yi haƙuri wanda bai gamsu su ba ya ja Allah ya isa ko ya bar wa Allah wanda shi ne babban mai hukunci ga dukkan talikai kuma ya na ba wa wanda ya so matsayi ya kuma sauke wanda ya iso.

Kazalika wanda ya gamsu da hukunci ya kan iya yi wa kotun kirrai a lokacin da kotun “ALLAH YA YI ALBARKA” don shari’a ta kaya bisa muradin sa ko ya yi nasara an ce shi ke da gaskiya. Duk maganar nan ta shafi sakamakon shari’ar zaɓen shugaban Nijeriya ne na 2023 inda kotun ba ta ɓata lokaci ba a zama biyu kacal ta yanke hukunci inda ta tabbatarwa shugaban da ke gado Bola Ahmed Tinubu nasara.

Kotu dai ba a yi ma ta shisshigi da nuna ga irin hukuncin da a ke ganin za ta yanke amma in mu ka bi tarihi a baya tun fara mulkin dimokraɗiyya a jamhuriya ta farko da ta kare da juyin mulkin da a ka zubar da jini a ranar 15 ga Janairu 1966, kotu ba ta taɓa sauke shugaban da ke gado ba. In an tuna ai a zaɓen tazarce na marigayi Shehu Shagari 1983 an samu waɗanda su ka nuna ƙin amincewa da sakamakon.

Cikin ƙaddara sojoji su ka kifar da mulkin farar hula inda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari lokacin ya na soja ya hau karaga kafin sojoji su yi ta mulki har 1999. A dai tsarin mulki kuma a gwamnatin farar hula akwai sassa uku masu riƙse da gwamnati da su ka haɗa da sashen zartrawa, sashen shari’a da kuma majalisa.

Ta kan yiwu sasahen zartarwa ya fi sauran ƙarfi musamman a Nijeriya don yadda shugaba ke da tasiri wajen samar da shugabannin majalisa da ma cankowa ko tabbatar da wanda zai zama babban alƙali da ke jagorantar Kotun Ƙoli. Daga siyasar 1999 da a ke ciki yanzu kimanin shekaru 25 an samu tunanin gara ka lashe zaɓe ko yaya in ya so a kai kai kotu don za ka iya samun nasara a kotu.

Shi ya sa wasu ’yan siyasa ke bin ta kowane hali su haye madafun iko bayan nan in an shiga kotu su ɗau manyan lauyoyi don kare muradun su. An ma taba samun lokacin da rundunar tsaron farin kaya ta cafke wasu alƙalai don tuhumar su da zarmiya. Haƙiƙa wuƙa da nama da tsarin mulki ya ba wa alƙalai kan iya zama mai amfani ko akasin haka bisa gaskiya ko rashin ta a tsakanin alƙalan.

Ba ma alkalai kaɗai ba hatta lauyoyi an zargin su da kawo cikas ga tabbatar da adalcin shari’a. Aƙalla su ma lauyoyin a wani lokacin an so cafke wasu daga cikin su da zargin haɗa kai ga baragurbi a tsakanin alƙalai don murde shari’a. Ba a jan zare sosai wajen batun kama alƙalai ko binciken lauyoyi sai maganar ta mutu. Irin wannan in ya faru wasu kan yi ca akan su ce a na neman firgita sashen shari’a ne ko ma a na zagon ƙasa ga ɗaya daga tubalan dimokraɗiyya ko tabbatar da adalci.

Wani lauya ya shaida min matuƙar za ka iya ɗaukar wasu manyan lauyoyi to za ka iya samun nasara a ƙarar da ka shigar ko a ka shigar da kai. Lauyan ya ƙara da cewa wasu alƙalan ka iya zama ’yan ajin makaranta ɗaya da lauyoyin ko ma lauyoyin iyayen gidan su ne. Manyan lauyoyi kan zama ciko ido ga alƙalai kuma kowa ya san akwai manyan lauyoyin da a kan tinkara in a na son samun nasarar shari’a. In ba mutum hamshaƙin mai hannu da shuni ba ne ba zai iya biyan kuɗin kafin alƙalamin ɗaukar irin waɗannan manyan lauyoyin ba. Manyan lauyoyin kamar bokaye su ke don in ka biya su kuɗin aiki to za ka iya komawa gida ka yi ajiyar zuciya don ka kama dahir indai ba wani hukuncin Allah ba.

Mu duba misalin lokacin tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ja da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ko a ce kotun ɗa’ar jami’an gwamnati ta thume shi da rashin ambata dukiyar sa tun lokacin ya na kujerar gwamnan jihar Kwara. Wannan qara ta kai ga har Kotun Ƙoli inda ƙarshe Bukola Saraki ya samu nasara kuma a hakan ya ciccije har ya kammala wa’adin shugabancin majalisa ta 8 ta dattawa. Labari ya zo cewa Bukola ya dauki ruwan manyan lauyoyi da su ka yi tsayin daka wajen kare shi har ya cimma gaci.

A gaskiya a lokacin alamu na nuna in ba don sanin logar Nijeriya ba da shige da fice da ruwan fitina ya yi awun gaba da Bukola. Mu sake tunawa da ruwan da ya yi awun gaba da babban alkali Walter Nkanu Onneghen inda shi ma a ka tuhume shi da rashin ambata kadarorin sa ko dukiyar sa da gano maqƙudan kuɗi a asausun san a banki. Haka dai da lamarin ya yi zafi a ka buƙace shi da ya yaɗa ƙwallon mangwaro don ya huta da ƙuda.

A wannan lokacin tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta naɗa tsohon alƙali Muhammad Tanko wanda shi ma bayan wani lokaci aka ce ya yi murabus bisa dalilan rashin ƙoshin lafiya duk a na raɗe-raɗin duk abun da ka ga ya koro vera ta faɗa wuta to ya fi wutar zafi. Akwai misalai da dama na rahotannin gidan shari’a ciki kuwa har da kama wasu ’yan sanda da a ka ce ko ma na bogi ne da shiga gidan tsohuwar alƙalin Kotun Ƙoli Mary Odili a anguwar Maitama inda su ka jidi maƙudan kuɗi da sunan gudanar da bincike.

Kotu ta nuna bakin ciki da hakan da jajantawa Mary Odili da buƙatar lalle a gudanar da gagarumin bincike don gano wanda ya ba da umurnin gudanar da binciken. Sharhin dai a nan na nuna yanda a ka samu wadannan makudan kuɗin a gida tun da nan din ba banki ba ne. Kazalika shin waɗanda su ka je kwasar kuɗin a ina su ka samu labari? Gaskiya labarin ya kawo tada jijiyar wuya sosai da jawo bacin ran kotun cewa an yi yunƙurin cin zarafin alƙalai ne.

Alqalin Kotun Ƙoli Jotis Musa Dattijo wanda ya yi ritaya ya caccaki yanayin shugabanci ko iko marar iyaka ga babban alƙalin kotun.

Dattijo Muhanmmed wanda ya yi aiki tsawon shekaru 47 a sashen shari’a ya yi ritaya inda masu ruwa da tsaki na ƙasa su ka halarci liyafar bankwana da da a ka shirya ma sa.

Dattijo ya nuna a duk inda a ka tarawa wani mutum ɗaya dukkan mukami to zai iya afkawa cikin zarmiya.

A nan dattijo ya ce misali matsayin mataimakin babban alƙalin wanda shi ma ya tava riƙe mukamin a matsayin mataimaki irin na siyasa ta yadda wanda ke kan kujerar sai in ya na so za ka yi tasiri.

Tsohon alqalin ya kawo misalan hukunci biyu da kotun ta yanke masu ban mamaki wajen ba wa tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan nasarar tikitin majalisar dattawa kan Bashir Macina duk da shi takarar tikitin shugaban ƙasa a APC ya tafi sai kuma nasara ga gwamnan Imo Hope Uzodinma wanda ya zo na huɗu a zaven da a ka ba shi nasarar.

Bayanan na Dattijo sun ɗauki hankalin jama’a.

Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen Nijeriya na 2023 Atiku Abubakar ya ce dalilin kashe jami’an ‘yan sanda 9 da ke gadin gidan sa a Kaduna ya sa shi gudun hijira na tsawon watanni.

Atiku na magana ne a helkwatar jam’iyyar PDP kuma a martanin sa na farko kan sakamakon ƙarshe na kotun koli kan ƙarar da ya shigar ta kalubalantar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

In za a tuna kotun ta tabbatarwa Tinubu nasara inda ta kori karar ta Atiku na PDP da Peter Obi na Leba.

Atiku ya ce ya zaɓi bin hanya mai wuya don raya dimokraɗiyya maimakon bin sauƙi da ba daraja.

Hakanan ɗan takarar wanda ya yi takarar shugaban ƙasa har sau 6 ya ce ya na nan zai cigaba da aiki don samun nasarar ƙarfafa dimokraɗiyya.

A nan Atiku ya ce matasa na da rawar takawa fiye da dattawa ‘yan uwan sa a wannan gwagwarmaya.

Kammalawa;

Koma dai me za a ce haƙiƙa duk ƙasar da ka ga ta samu cigaba wajen bin doka da oda to sai an samu jami’an tsaron ta na da amana inda kotuna kuma ko alƙalai za su zama masu adalci wajen yanke hukunci na adalci ba tare da la’akari ga duk wanda sandar shari’a za ta hau kan sa ba. Ma’ana adalcin shari’a kar ya bambance ’yan bora da ’yan mowa.

Hatta magudin zaɓe ma ka iya karewa ko zama tarihi matuƙar kotuna na nan don ba wa maigaskiya gaskiyar sa wanda ya zarme kuwa ya fuskanci hukunci. A na su bangaren ’yan siyasa kuma har dai sun san ba su da gaskiya to su guji tinkarar kotu in kuma su ka tinkara kuma su ka rasa nasara to bai daidai ba ne su ja Allah ya isa ga kotun Allah ya isa!

By Editor